Gwamna Ya Kauracewa Gidan Gwamnati, Ya Koma Tafiyar da Mulki Daga Cikin Gidansa
- Gwamnan Alex Otti ya kauracewa gudanar da aiki a gidan gwamnatin Abia inda ya koma yin aiki daga gidansa na Nvosi Umuehim
- Gwamnan ya ce ba zai iya yin aiki a gidan gwamnatin jihar ba saboda ya lalace kuma ko kadan ginin bai dace da tsarin Abia ba
- Sai dai Gwamna Otti yi alkawarin gina “gidan gwamnati da ya dace” kafin karshen shekara, yayin da zai ci gaba da aiki daga gidansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abia - Gwamna Alex Otti na Abia ya bayyana dalilin da ya sa yake gudanar da aiki daga gidansa na Nvosi Umuehim, yana mai cewa jihar ba ta da gidan gwamnati mai kyau.
Gwamna Otti ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Arochukwu, yayin da yake kaddamar da sabon ofishin shugaban karamar hukumar Arochukwu (LGA) da aka gina.
Tarihin matsalar gidan gwamnati a Abia
Jaridar Tribune ta ruwaito gwamnan ya bayyana cewa ya kauracewa gudanar da aiki a gidan gwamnatin jihar ne saboda lalacewar gine-ginen gidan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce gwamnatocin da suka shude a jihar sun fara gudanar da ayyukansu ne daga ofishin haya, wadanda akasarinsu sun lalace.
Gwamnatocin baya na Sanata Theodore Orji da Dakta Okezie Ikpeazu sun fara gina gidan gwamnati a Layout Ogurube amma Otti ya ce ginin ba shi da inganci kuma bai dace da jihar ba.
Otti zai gina sabon gidan gwamnati
Don haka, Otti yi alkawarin gina “gidan gwamnati da ya dace” kafin karshen shekara, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
"A yau, ba na aiki daga gidan gwamnati da ke Umuahia saboda babu gidan gwamnati. Ko ina ya lalace kuma yayin da wasu bangarorin suka rube.
Zabin dai shine in yi amfani da kudin da nake biyan ‘yan fansho da shi domin sake fasalin gidan gwamnati. Amma na zabi yin aiki daga cikin gidana domin dakile hakan.
"Amma a yanzu ina alfaharin sanar maku cewa kafin karshen shekara, za mu rusa wadancan gine-ginen da suka lalace, mu gina gidan gwamnati da ya dace da Abia."
- A cewar Gwamna Otti.
Osun: Adeleke ya shiga gidan gwamnati
A wani labarin, mun ruwaito cewa bayan shafe shekara daya da watanni hudu da karbar rantsuwa, Gwamna Ademola Adeleke ya shiga gidan gwamnati.
Gwamnan kafin shiga gidan gwamnatin ya na rayuwa ne a gidansa da ke Ede, wani kauye kusa da birnin Osogbo a jihar Osun inda yake tafiyar da mulkinsa daga can.
Asali: Legit.ng