'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Zo da Sabon Ta'addanci, Sun Yi Barna a Ofishin 'Yan Sanda

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Zo da Sabon Ta'addanci, Sun Yi Barna a Ofishin 'Yan Sanda

  • Ƴan ta'adda da ake kyautata zaton mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai farmaki kan ofishin ƴan sanda a jihar Borno
  • Miyagun sun hallaka mutum biyu tare da ƙono motocin sintiri guda biyu da wani babur na jami'an tsaron
  • Sun kuma yi awon gaba ba da makamai bayan sun kwashe sa'o'i suna fafatawa da jami'an tsaron a cikin dare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Wasu ƴan ta’adda da ake kyautata zaton ƴan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai farmaki ofishin ƴan sanda na Jakana da ke ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno.

Ƴan ta'addan a yayin da suka kai harin sun kashe ɗan sanda direba tare da wata mace guda ɗaya.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Minista ya yi magana mai kaushi, ya fadi kulla kullar da ake yi

'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
'Yan ta'addan Boko Haram sun farmaki ofishin 'yan sanda a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan Boko Haram sun farmaki ƴan sanda

Ƴan ta’addan sun kuma ƙona wasu motocin sintiri biyu na ƴan sanda da ƴan sa-kai na CJTF da wani babur guda ɗaya, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan ta'addan sun kuma yi awon gaba da wasu makamai da alburusai a yayin harin da suka kai ofishin ƴan sandan.

Garin Jakana wanda yake a kan titin Damaturu-Maiduguri yana da nisan kilomita 45 daga birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wata majiya mai tushe ta ce ƴan ta’addan sun kai farmaki ofishin ƴan sanda ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, inda suka yi artabu da jami’an tsaro na tsawon sa'o'i uku, suka ci ƙarfinsu, sannan suka tafi da wajen misalin ƙarfe 3:00 na dare.

Me hukumomi suka ce kan harin?

Shugaban ƙaramar hukumar Konduga, Abbas Ali Abari, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho, sai dai bai bayar da cikakkun bayanai ba.

Kara karanta wannan

Matasa na shirin zanga zanga, jami'an tsaro sun harbe ƴan fashi har lahira

"Eh na samu kira kan cewa ƴan ta’addan Boko Haram sun hari ofishin ƴan sanda na Jakana jiya da daddare. Ina magana DPO, kuma da zarar na samu cikakkun bayanai zan sanar da ku."

- Abbas Ali Abari

Legit Hausa ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Nahum Daso, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya tabbatar da lamarin inda ya ce jami'an ƴan sandan sun yi nasarar daƙile harin da ƴan ta'addan suka kai.

ASP Nahum Daso ya tabbatar da cewa an kashe jami'an ɗan sanda ɗaya mai muƙamin sufeta tare da wata farar hula mutum ɗaya.

Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hari

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari babban titin Maiduguri zuwa Kano.

Bayanai sun nuna cewa ƴan ta'addan sun kwashi fasinjoji da dama sun yi awon gaba da su zuwa wurin da ba'a sani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng