Matakan Gaggawa 10 da Gwamnatin Tinubu Ta Dauka Daga Jin Za a Shirya Zanga Zanga
Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi duk abubuwan da za ta iya domin ganin ta hana a shiga zanga-zangar lumuna a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Gwamnatin tarayya ta bi hanyoyi iri-iri da kuma wasu dabaru da matakai da ake ganin an nufe su ne domin shawo kan matasan kasar.
Legit Hausa ta jero wadannan matakai da tsare-tsare da aka fito da su a gurguje:
1. Karin albashin ma’aikata
Duk da an yi watanni ana tattaunawa, gwamnatin tarayya ta yi maza ta kara mafi karancin albashi daga N38, 000 zuwa N70, 000 a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin a ce kobo, shugaban kasa ya tsaida magana kuma ya kai kudiri gaban ‘yan majalisa, su ma ba su bata lokaci ba suka amince da batun.
2. Tinubu ya zauna da ‘yan kwadago
Shugaba Bola Tinubu ya yi kokarin zama da ‘yan kwadago domin su amince da karin, kuma ya yi masu wasu alkawura ya shawo kan su.
Wannan ya taimaka wajen hana ‘yan kwadago ba zanga-zangar karfi, wanda hakan ya na iya kai wa ga yin yajin-aiki da zai mamaye kasar.
3. Zanga-zanga: Taron Shugaban kasa da malamai
An rahoto yadda gwamnatin tarayya ta yi zama da malaman addini da nufin a hana matasa hawa tituna da sunan zanga-zangar lumana.
Malamai sun yi ta kokarin yin wa’azi a mimbari domin fadakar da matasa da gwamnati.
4. Tinubu ya hadu da Sarakuna kan zanga-zanga
Shugaban kasa ya sa an kira masa sarakunan gargajiya inda ya lallabe su kan batun. George Akume ya wakilce shi a zaman da aka shirya.
5. Rabon kudi da tallafi
A ‘yan kwanakin nan aka aji gwamnatin tarayya ta fara rabon shinkafa. Tuni dai tireloli sun isa wasu jihohi da nufin rage yunwar da ake yi.
Premium Times ta ce gwamnati ta fitar da sama da N438bn a rabawa Abuja da jihohi 34 a karkashin NG-CARES domin rage talauci.
6. Ministocin Tinubu sun tashi tsaye
Ministoci su na ta kokari wajen gamsar da al’umma cewa an fito da tsare-tsare da za su magance matsin rayuwa da kuncin da ake ciki a yau.
7. Tallafin kudi ga matasa
Ana haka ne kuma aka ji Ministar cigaban matasa, Dr. Jamila Ibrahim Bio ta ce kwanan nan za a fito da tsarin rabon tallafin N110bn ga matasa.
Jamila Bio ta ce an fito da shirin YIF ne da nufin tallafawa matasa da jarin Naira biliyan 100 domin inganta sana'o'i da kuma tattalin arziki.
8. Gwamnatin tarayya ta raba jari
A jihar Jigawa, an ji yadda gwamnatin Tinubu ta raba N50, 000 ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa a karkashin jagorancin Kashim Shettima.
9. Lamunin karatu zai hana zanga-zanga?
Maganar lamunin karatu yana neman ya tabbata bayan an dade ana je-ka-ka-dawo, ana tunanin hakan zai iya kwantar da hankalin dalibai.
10. Sadaukar da rabin albashin ‘yan majalisa
Su kuwa ‘yan majalisar wakilan tarayya sun sadaukar da rabin albashin da ake biyansu a wata duk saboda ganin an biyawa jama’a bukatunsu.
‘Yan majalisar sun ba da shawarar a zauna da matasa domin a hana su hawa tituna.
An nemi a hakura da zanga-zanga
Rahoton nan ya nuna cewa Kashim Shettima ya ba ƴan Najeriya shawarar su yi watsi da maganar shirya zanga-zangar lumana a Najeriya.
Mataimakin shugaban ƙasan ya buƙaci a haƙura da fitowa kan tituna yin zanga-zanga, ya nuna cewa yanzu ba lokacin yin hakan ba ne ko kaɗan.
Asali: Legit.ng