Zanga Zanga: Bayan Gargadin Malaman Musulunci, Kungiyar CAN Ta Fadi Matsayarta
- Kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN ta bi sahun malaman Musulunci wurin hani da fita zanga-zanga a fadin kasar
- Kungiyar ta ce duk da ana shan wahala da tsadar rayuwa da kuma rashin tsaro, akwai hanyoyin korafi da dama
- Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan malaman Musulunci sun gana da Bola Tinubu kan halin da ake cikin da kuma zanga-zanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) ta fadi matsayarta kan shirin zanga-zanga.
Kungiyar ta gargadi matasa kan fita zanga-zanga inda ta ce sulhu shi ne mafita wurin dakile matsalar.
Zanga-zanga: Kungiyar CAN ta ba da shawara
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Daniel Okoh ya fitar, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CAN ta bukaci ba gwamnati karin lokaci domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta madadin fita zanga-zanga.
Ta bayyana damuwa kan yadda miyagu ka iya amfani da wannan damar wurin kawo hatsaniya yayin zanga-zangar, Vanguard ta tattaro.
"Sulhu da korafe-korafe ta hanyar da suka sace da kuma ganawa su ne hanyoyin shawo kan matsalar ba tare da bin hanyar rigima ba."
"CAN tana tare da duka ƴan ƙasa a cikin wannan hali da ake ciki na tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki."
"Muna sane da kuma tausayawa al'umma ganin yadda ake fama da yunwa a fadin kasar da kuma rashin tsaro."
- Daniel Okoh
Kungiyar CAN ta ba gwamnati shawara
Daniel Okoh ya bukaci gwamnati ta rage yawan kashe kudi da take yi musamman a ofisoshin masu mukamai na siyasa.
Ya ce ya kamata a dakile almubazzaranci da masu rike da mukamai ke yi domin nuna damuwa kan halin da ake ciki
Malaman Musulunci sun gana da Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa malaman Musulunci sun samu yin wata ganawa da Shugaban Bola Tinubu kan mawuyacin hali da ake ciki.
Malaman suka ce sun fadawa shugaban gaskiya kan halin da ake ciki musamman tsadar rayuwa da kuma tashin tsaro a kasar.
Hakan bai rasa nasaba da shirin fita zanga-zanga da matasa ke yi a kasar a farkon watan Agustan 2024 da za mu shiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng