Matashi Ya Balle Kofar Masallaci Ya Saci Wayar N100,000, an Gurfanar da Shi Gaban Kotu
- Matashi mai shekaru 19 mai suna Karim Sodiq ya shiga hannun hukuma bayan ɓalle masallaci tare da sace wayar salula
- 'Yan sanda sun gurfanar da saurayin a gaban wata kotun majistare da ke Ibadan inda ya musanta aikata laifuffukan da ake zarginsa
- Ɗan sandan da ya kai shi kotun ya ce matashin ya ɓalle kofar masallacin ne a ranar 21 ga Mayu wurin ƙarfe 7:50 na yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ibadan - Jami'an 'yan sanda a ranar Juma'a sun gurfanar da wani matashi mai shekaru 19 a duniya mai suna Karim Sodiq.
An gurfanar da shi ne a gaban wata kotun majistare dake Ibadan kan zarginsa da sace wayar zamani a cikin Masallaci.
Sodiq, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, ana zarginsa ne da sata tare da balle kofar masallaci, tuhume-tuhume da ya musanta aikatawa, jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ɓalle Masallaci - Sifeta Adeshina Folaranmi
Jami'i mai shigar da kara, Sifeta Adeshina Folaranmi, ya sanar da kotun cewa wanda ake karar ya aikata laifin a ranar 21 ga watan Mayu wurin ƙarfe 7:50 na yamma.
Sifeta Folaranmi ya shaidawa kotun cewa matashin ya ɓalle kofar masallacin ne a Oju-Aba da ke yankin Moniya a Ibadan.
Jami'in ya ce wanda ake karar ya kutsa cikin masallacin inda ya sace wayar zamani ƙirar Infinix Smart 6 da kudinta ya kai N100,000 mallakin wata Akorede Suliyat.
Ya ce waɗannan laifuffukan da Sodiq ya aikata sun ci karo da sashe na 415 da na 390(9) da ke a dokokin laifukan jihar Oyo na 2000, rahoton Daily Post.
Alkalin majistaren, Ayorinde Ayo-Alagbe, ya bayar da belin wanda ake zargin kan N200,000 tare da waɗanda zasu tsaya masa mutum biyu.
An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 15 ga Agustan 2024.
'Yan bindiga sun kai hari wurin ibada
A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki wani wurin bauta dake jihar Kwara.
An gano cewa 'yan sandan dake sintiri tare da haɗin guiwar 'yan banga ne suka cece mutanen, duk da dai an samu wasu sun ji rauni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng