An gurfanar da wanda ya sace wayar alƙaliya a kotu

An gurfanar da wanda ya sace wayar alƙaliya a kotu

Rundunar ƴan Sandan Jihar Ebonyi a ranar Juma'a ta gurfanar da wani Obiemezie Chiekezie gaban kotun gargajiya da ke zamanta a Abakaliki kan sace wayar wata alƙaliya.

Alƙaliyar, Mrs Ezeugo Esther ta fita motsa jiki da safe ne misalin ƙarfe 5.30 na asuba a Nna Street inda wanda ake zargin ya fizge wayan daga hannunta ya tsere.

An yi ƙoƙarin bin sahunsa a ranar amma ba ayi nasara ba har sai ranar Laraba da ƴan sanda suka gano shi.

An gurfanar da wanda ya sace wayar alkali a kotu
An gurfanar da wanda ya sace wayar alkali a kotu. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: An kama wani magidanci da ke luwadi da kananan yara a Bauchi

An gurfanar da Chiekezie a ranar Juma'a a kan tuhumarsa da yin sata.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara ya shaidawa kotu cewa laifin ya ci karo da sashi na 402(A) na Criminal Code Cap. Vol. 33, Vol. 1 na dokokin jihar Ebonyi ta Najeriya, 2009.

Ba a shigar da buƙatar neman beli ba duba da cewa babu lauya mai kare wanda ake zargin a kotun.

Amma a yayin yanke hukunci, shugaban Kotun, Mrs Nnenna Onuoha ta bayar da belinsa kan kudi Naira miliyan 1 da mutum ɗaya da zai tsaya masa.

A cewar ta wanda zai tsaya masa sai ya kasance yana da gida/fili a kusa da kotun tare da gabatar da sahihan takardun gidan.

Ta dage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 27 ga watan Yulin shekarar 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164