Asirin wani barawon masallaci ya tonu, duba hukuncin da kotu ta yanke masa

Asirin wani barawon masallaci ya tonu, duba hukuncin da kotu ta yanke masa

A yau, Laraba ne wata kotun Grade 1 da ke zamanta a Aso-Pada, Mararaba a jihar Nasarawa ta yanke hukuncin shekaru 2 a gidan yari kan wani matashi mai shekaru 27, Musa Abubakar saboda samunsa da laifin satar janareto na massalaci.

Alkalin kotun, Yusuf Yaqub ya bayyana cewa ya yanke wa Abubakar hukuncin zuwa gidan yari ne saboda hujjoji da aka gabatar a kansa da kuma amsa laifin da ya yi.

Yaqub ya ce kotu ya yanke wa Abubakar hukuncin zaman yari na shekaru daya ko ya biya tarar N5,000 na laifin shiga cikin masallacin domin aikata sata sannan ya kuma yanke masa hukuncin shekara daya na yunkurin sata kuma ba tare da zabin biyan tara ba.

Asirin wani barawon masallaci ya tonu, duba hukuncin da kotu ta yanke masa
Asirin wani barawon masallaci ya tonu, duba hukuncin da kotu ta yanke masa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya yi murabus bayan ya zargi gwamnati da almundaha

Abubakar wanda ba'a bayar da adireshinsa ba ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa inda ya roki kotu tayi masa sassauci.

Da farko, dan sanda mai shigar da kara, Saja Agabi Auta ya shaidawa kotu cewar wani Abdullazeez Yusuf da ke zaune a Aso C, Maraba ne ya shigar da karara a cajo ofis da ke Maraba a ranar 8 ga watan Oktoba.

Auta ya shaidawa kotu cewa a ranar 8 ga watan Oktoban ne wanda ake kara ya sullale ya shiga Masallacin unguwa inda ya balle kofar inda ake ajiye janarator yana kokarin ficewa da ita amma sai wani ya hango shi.

Saja Auta ya shaidawa kotu cewar a baya an taba samun Abubakar da laifin satar Amplifier a wani masallaci da ke tashan motocci na Gombe Line a Maraba.

Ya ce laifukan sun ci karo da sashi ne 354 da 95 na Penal Code.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164