Bayan Rasuwar Sulaiman Alaka, an Yi Rashin Furodusa Kuma Jarumin Fina Finai
- Masana'antar shirya fina-finan Nollywood ta tafka babban rashin jarumi kuma furodusa, Charles Owoyemi
- An tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne tun a ranar Juma'a 19 ga watan Yulin 2024 bayan ya sha fama da jinya
- Abokan aikin marigayin su suka bayyana haka a jiya Alhamis 25 ga watan Yulin 2024 inda suka yi masa addu'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - An tafka babban rashin a masana'antar Nollywood bayan rasa wani jarumin fim kuma furodusan fina-finai.
Marigayin mai suna Charles Owoyemi ya rasu ne a ranar Juma'a 19 ga watan Yulin 2024 bayan ya sha fama da gajeruwar jinya.
Owoyemi: Yaushe jarumin fina-finan ya rasu?
Abokan aikinsa, Tunji Bamishigbin da Ralph Nwadike su suka bayyana haka a jiya Alhamis 25 ga watan Yulin 2024, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu bayanan rasuwar marigayin ne bayan kwanaki shida ba tare da sanin musabbabin mutuwar tasa ba.
Rahotannin sun tabbatar da cewa marigayin bai cika fitowa wurin bayyana kansa ko kuma hira da 'yan jaridu ba.
Yadda marigayin ya gamu da jarabawa
Ana zargin rashin lafiyar marigayin na alaka da koma baya da ya samu a masana'antar bayan cigaban da aka samu, The Nation ta tattaro.
"Cikin jimami da kuma takaici muke sanar da mutuwar babban abokinmu kuma amininmu, Charles Owoyemi."
"Marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a 19 ga watan Yulin 2024 bayan ya sha fama da jinya."
- Cewar sanarwar
Abokan aikin nasa sun yi addu'ar samun rahama gare shi da kuma hakurin jure rashin aminin nasu daga bangaren iyalansa.
Marigayin ya shirya wasu fina-finai ciki har da 'Village Head Master' wanda ya rubuta zangon da ke dauke da kashi 50.
Shugaban Ohanaeze Ndigbo ya kwanta dama
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kungiyar kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, Cif Emmanuel Iwuanyanwu ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya rasu ne a jiya Alhamis 25 ga watan Yulin 2024 bayan ya sha fama da jinya kamar yadda dansa, Jude Iwuanyanwu ya sanar.
Asali: Legit.ng