Kwamishina Ya Fadi Maƙudan Kuɗin da Gwamnatin Kano Ke Buƙata Domin Gyara Makarantu
- Kwamishinan ilimin Kano, Umar Doguwa, ya bayyana cewa ana bukatar Naira biliyan 60 domin gyara bangaren ilimi a jihar
- Umar Doguwa ya ce ɗaliban makarantun gwamnati a jihar wurin miliyan 4.5 ne ke zama dirshan a kasa yayin koyon karatu
- A zantawarmu da wasu daga cikin jama'ar Kano kan wannan ci gaba, sun yabawa kokarin Gwamna Abba da ke shirin ceto ilimi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnatin Kano a ranar Alhamis ta bayyana cewa tana buƙatar kusan Naira biliyan 60 domin gyara makarantun da suka lalace a jihar
A cewar gwamnatin, hakan zai kawo ƙarshen zaman da ɗalibai suke yi daɓas a ƙasa a makarantu da dama.
Daliban Kano miliyan 4.5 na zaman kasa
Kwamishinan ilimi na jihar, Umar Doguwa, ya bayyana hakan a wata zantawa da yayi da manema labarai a Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano a halin yanzu tana kula da ɗalibai miliyan 7 a makarantun firamare da sakandare a faɗin ƙananan hukumomi 44 a jihar.
Kwamishinan ya ce:
"Jihar a halin yanzu tana lura da makarantun gwamnati 10,000 waɗanda sama da ɗalibai miliyan 4.5 ne ke karatu a ƙasa."
"Gwamnatin Ganduje ta lalata ilimi" - Doguwa
Umar Doguwa ya ce rufe wasu makarantu da gwamnatin da ta gabata tayi ya bada gudumawa wurin lalacewar ilimi a jihar.
Kwamishinan ya yabawa Gwamna Kabir Yusuf kan ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi tare da ƙara yawan kasafin kudi a bangaren ilimi da kusan kashi 30.
Gwamnati tana neman N60bn a Kano
Ko a shekarar 2023, PM News ta ruwaito Umar Doguwa ya shaidawa UNICEF cewa gwamnatin Kano na neman jarin N60bn daga masu ruwa da tsaki domin gyara makarantu.
Ya tabbatar da shirin da ke kan hanya na tabbatar da tsarin ilimi mai kyau a jihar da fatan hakan zai shawo kan matsalolin bangaren.
Legit ta tattauna da mazauna Kano
A zantawarmu da wasu mazauna Kano, sun bayyana gamsuwarsu kan kokarin gwamnatin Kano na gyara ilimi musamman ganin yadda makarantu suka dade ba tare da gyara ba.
Abba Hassan Gezawa ya ce tun zamanin kwamkwaso da aka rika yiwa makarantun gwamnati gyara, ba a kara waiwayar makarantun ba sai a wannan gwamnatin.
Abba Gezawa ya ce yana fatan Abba Kabir Yusuf zai kwaikwayi ubangidansa Rabiu Musa Kwankwaso wajen gyara makarantu, daukar nauyin dalibai marasa galihu a jihar.
Ismai'il A.T.O ya ce abin bakin ciki ne idan ka je wasu makarantun firamare da sakandare na jeka ka dawo a jihar yadda suke zama a kasa, ko kuma wasu ajujuwan an daina amfani da su saboda sun lalace.
Ismail ya ce yana fatan idan gwamnatin jihar ta samu kudin da take nema, ta fi mayar da hankali kan makarantun firamare inda nan ne tushen karatun yara yake.
Abba zai yi garambawul a harkar ilimi
A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar ba-zata wata makarantar gwamnati inda ya ga abun mamaki.
Gwamnan ya tarar da ɗalibai mata na zaune a kasa a kwalejin kimiyya a jihar, a take yayi alkawarin yin gyaran da zasu mora.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng