Tsadar Burodi: Gwamnatin Kano ta Shiga Ganawa Domin Ganin Samun Sauki Inji PCACC
- Gwamnatin Kano ta shiga cikin matsalar hauhawar farashin burodi da wasu daga cikin mazauna jihar su ke korafi a kai
- Shugaban hukumar karbar korafe-korafe ta Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce sun nemi zama da masu sayar da fulawa
- Haka kuma Rimin Gado ya shaidawa jaridar Legit cewa za su zauna da masu buga burodin domin gano inda aka samu akasi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Hukumar karbar korafe-korafe ta Kano (PCACC) ta gayyaci dilolin fulawa da ke kasuwar Singa da masu gidajen burodi a kan hauhawar farashin burodi.
Shugaban hukumar, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya mikawa masu ruwa da tsaki a bangaren samar da burodi gayyatar biyo bayan korafe-korafe da jama'ar gari.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Barista Muhyi Magajo Rimin Gado ya ce daga cikin ayyukansu akwai yaki da rashawa da kuma duba korafin jama'ar gari domin samar da mafita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Za mu gano dalilin tsadar burodi," Muhyi
Shugaban hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce za su zurfafa bincike domin gano musabbabin tsadar burodi a fadin jihar.
Solace Base ta wallafa cewa Barista Rimin Gado ya ce wannan na daga cikin aikin hukumarsa kamar yadda ya ke a cikin sashe na tara da na 15 na dokar hukumar na shekarar 2008 da aka yi wa kwaskwarima.
PCACC na fafutukar saukar farashin burodi
Hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta shaidawa Legit Hausa cewa za ta zauna da duk wanda ya kamata wajen sauko da farashin burodi.
Ya shaidawa Legit cewa dole su bi kadun lamarin domin kawo sauki, inda ya ce yanzu haka sun gayyaci wadanda su ka dace, kuma akwai yiwuwar su gayyaci masu masana'antun fulawa.
Farashin burodi ya tashi a jihohi
A wani labarin, an ji an samu tsadar burodi da karancinsa a wasu yankunan jihohin Kano da Kaduna da Katsina, wanda ya sa jama'a ke ganin za su iya daina sayensa.
Masu gidajen burodi dai sun yi korafin cewa farashin buhun fulawa ya koma N70,000 daga N63,000 da su ke saya, saboda haka su ka ce dole su kara kudin burodi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng