NYSC: Tinubu Zai Ƙarawa Matasa Masu Bautar Ƙasa Alawus? Abu 3 da Ya Kamata Ku Sani
- Gwamnatin Bola Tinubu na iya karawa matasa masu bautar kasa alawus bayan amincewa da sabon mafi karancin albashi na N70,000
- Tinubu ya mikawa majalisar tarayya kudurin dokar sabon mafi karancin albashin na N70,000 bayan cimma matsaya da 'yan kwadago
- Matakin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka a baya da kalaman Godswill Akpabio na nuni da yiwuwar karawa 'yan NYSC alawus
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana sabon mafi karancin albashi na N70,000. Tuni majalisar tarayya ta amince da kudurin.
Sakamakon wannan ci gaba, ana kyautata zaton Shugaba Tinubu zai karawa masu yiwa kasa hidima (NYSC) alawus na wata-wata daga N33,000 zuwa N70,000 (sabon albashi).
A yayin da Najeriya za ta koma amfani da N70,000 matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata, ga wasu dalilai da ka iya sa 'yan NYSC su samu karin alawus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NYSC: Buhari ya kara alawus zuwa N33,000
Idan ba a manta ba, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kara alawus din matasan zuwa N33,000 bayan ta kara mafi karancin albashi zuwa N30,000 a shekarar 2019.
Duk da cewa tsohon shugaban kasa Buhari ya amince da mafi karancin albashi a ranar 18 ga Afrilu, 2019, sabon alawus na 'yan NYSC ya fara aiki ne a watan Janairun 2020 kuma an sanya shi a cikin kasafin shekarar.
Idan Tinubu zai kwaiwakyi magabacinsa, gwamnatinsa na iya sanya sabon alawus ga matasa masu yi wa kasa hidima a cikin kasafin kudin 2024.
Hukumar NYSC tayi nuni ga sabon alawus
Har ila yau, shugaban hukumar NYSC, Birgediya Y.D Ahmed ya ce da yiwuwar gwamnatin Tinubu ta hada da matasan a sabon mafi karancin albashi.
Birgediya Ahmed ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai sansanin masu yi wa kasa hidima na NYSC na jihar Ogun a ranar 6 ga watan Yuli.
Ya kuma yi nuni da masu bautar kasar na iya amfana da sabuwar yarjejeniyar mafi karancin albashi idan majalisar dokokin kasar ta amince da shi.
Jawabin Akpabio a kan sabon albashin
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yi nuni da cewa mafi karancin albashi na N70,000 ya shafi kowa da kowa, ciki har da direbobi, masu gadi, 'yan aikin gida da sauransu.
Ana ganin, wannan jawabin na shugaban majalisar dattawan alama ce mai karfi da ke nuni da cewa matasa masu yiwa kasa hidima na iya shiga sahun masu samun N70,000.
Sanata Akpabio ya ce:
“Idan kai tela ne kuma ka dauki mutane aiki, dole ka rika biyansu N70,000 ko sama da hakan. Idan kana da yar aikin gida, ko direba da mai gadi, ba za ka iya biyan su kasa da N70,000 ba.”
Gwamna ya dauki 'yan NYSC aiki
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Neja ya ɗauki matasa masu yiwa ƙasa hidima aiki, waɗanda suka karanci likitanci da sauran fannonin kiwon lafiya.
Mohammed Umaru Bago, ya sanar da cewa gwamnatinsa ta ɗauke su aiki ne domin kawo ƙarshen mutuwar likitoci da sauran malaman lafiya a Asibitocin Neja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng