Sabon tsarin mafi karancin albashi ya fara aiki a kan kananan Ma’aikata – Ngige

Sabon tsarin mafi karancin albashi ya fara aiki a kan kananan Ma’aikata – Ngige

Ministan kwadagon Najeriya, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta soma biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikatan da aka dade ana ta faman sa-in-sa a kai.

Dr. Chris Ngige yake cewa gwamnatin Najeriya ta fara ba ma’aikatanta wannan sabon karin albashi ne domin ta dauki karin da muhimmanci kamar yadda kungiyoyin kwadago su ka nema.

Ministan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi hira da Jaridar Daily Sun. “N30, 000 na karamin ma’aikaci na matakin karshe ne a wajen aiki, don haka mun fara biyan wannan kudi.”

Ngige ya kara da cewa: “Mun samu matsala ne a kan karin da za a yi wa wadanda ke mataki na 7 zuwa 14 wanda su ne Ma’ikatan da su ke karbar abin da ya haura sabon mafi karancin albashin.”

KU KARANTA: Albashin 'Yan Majalisar Wakilai da Sanatocin Najeriya

Ministan ya yi ikirarin cewa ana samun matsala wajen dabbaka sabon albashin ne wajen tattaunawar da ake cigaba da ya yi tsakanin gwamnati da kuma bangaren ‘yan kwadagon kasar.

“Duk abin da ya shafi albashi musamman idan tattalin arzikin kasa bai da kyau, zai zo da wahalar yarjejeniya.” Inji Ministan kamar yadda rahotanni su ka fito a Ranar 7 ga Watan Oktoban 2019.

A karshen hirar Ministan kwadago da aikin-yin na shugaba Muhammadu Buhari da Daily Sun, ya nuna cewa ya na sa rai za a kara albashin yadda zai shafe kowane matakin aikin gwamnati.

An samu sarkakiya wajen soma biyan albashin ne a dalilin gaza samun matsaya tsakanin kungiyoyin kwadago da jami’an gwamnati game da karin da za a yi wa manyan ma’aikatan kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng