Daga karshe Buhari ya fara biyan yan bautan kasa albashin N33,000

Daga karshe Buhari ya fara biyan yan bautan kasa albashin N33,000

Rahotanni sun tabbatar da cewa matasa masu yi ma kasa hidima sun fara samun sabon alawus na naira dubu talatin da uku (N33,000) kamar yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki alkawari.

A cikin wannan makon ne shugaban hukumar NYSC, Shuaibu Ibrahim ya sanar da karin kudin alawus din, inda yace yana sa ran nan bada jimawa ba gwamnati za ta fara biyan kudin bayan samun amincewa daga shugaban kasa.

KU KARANTA: An kashe mutane 3, an babbaka gidaje 20 saboda rikicin sarauta a jahar Kogi

Daga karshe Buhari ya fara biyan yan bautan kasa albashin N33,000
Daga karshe Buhari ya fara biyan yan bautan kasa albashin N33,000
Asali: Facebook

Sai ga shi kwatsam a ranar Alhamis yan bautan kasa sun fara samun sakon shigar kudi na bankuna dake tabbatar musu da sabon albashin, yan bautan kasa masu amfani da bankin Zenith ne suka fara samun kudin, yayin da sauran bankunan suka fara biya a ranar Juma’a, 31 ga watan Janairu.

Kafin wannan kari, yan bautan kasa suna amsan N19,000 ne a matsayin alawus dinsu na wata wata, shi ma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya yi musu wannan karin a shekarar daya kara karancin albashi zuwa N19,000.

Shi ma wannan kari da yan bautan kasa suka samu ya tabbatu ne biyo bayan rattafa hannu a kan sabon karancin albashi an N33,000 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, wanda tuni gwamnatin tarayya ya fara aiwatar da shi, da wasu jahohi.

Sai dai yayin da yan bautan kasa ke murnar samun wannan cigaba, wasu yan Najeriya suna ganin wannan ba wani abin farin ciki bane, saboda a cewarsu N33,000 bai kai canjin dala 100 a Najeriya ba.

A wani labari kuma, gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da sunan Malam Sani Dalhatu a matsayin sabon shugaban hukumar kulawa da jin dadin alhazai ta jahar Kaduna.

Kafin nadinsa, Malam Musa shi ne shugaban sashin ayyuka na hukumar jin dadin alhazai na jahar Kaduna, kuma ya dauki tsawon shekaru 20 yana aiki a hukumar alhazai.

Haka zalika Malam Musa ya taba zama shugaban kula da jin dadin alhazai a karamar hukumar Birnin Gwari, Igabi da wasu kananan hukumomi, kuma ya taba mai kula da shiyya domin jin dadin alhazai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel