Kwara: Miyagun 'Yan Bindiga Sun Farmaki Masu Ibada, 'Yan Sanda Sun Kai Daukin Gaggawa

Kwara: Miyagun 'Yan Bindiga Sun Farmaki Masu Ibada, 'Yan Sanda Sun Kai Daukin Gaggawa

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki wani sansanin masu ibada dake yankin Oluwalose a ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a Kwara
  • An gano cewa, wasu ma'auta da suka je yin ibada sansanin sun samu raunuka yayin da 'yan bindiga suka kai harin a safiyar Laraba
  • Rundunar 'yan sandan jihar Kwara sun tabbatar da faruwar lamarin amma sun ce tawagar sintiri sun hanzarta kai dauki a lokacin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani sansanin masu ibada da ke unguwar Oluwalose a karamar hukumar Ilorin ta Yamma a jihar Kwara.

An ce wasu ma'aurata sun samu raunuka a harin da 'yan bindigar suka kai sansanin ibadar da ke kan titin Okoolowo-Jebba a safiyar Laraba.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ta yi babbar barna a jihar Arewa, mutum 1,664 sun rasa matsugunni

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan harin 'yan bindiga a jihar Kwara
Kwara: 'Yan sanda sun dakile harin garkuwa da mutane a Ilorin. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi (DSP), ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindigar suka kai hari

A cewarta, masu garkuwa da mutane sun kutsa cikin sansanin Alfa Bukhari Jamiu Tunde inda suka yi yunkurin sace bakin da suka je yin ibada.

“Da isowarsu, an gano cewa wasu mutane tara dauke da bindigogi kirar AK-47 da kuma bindigun gargajiya, sun kutsa cikin sansanin da nufin yin garkuwa da baki.
“Amma Allah ya takaita lamarin bayan gaggawar mayar da martani da shiga tsakani da tawagarmu ta sintiri da ’yan banga suka yi. Ba ayi garkuwa da kowa ba."

- A cewar DSP Ejire-Adeyemi.

Jaridar Tribune ta ruwaito DSP Ejire-Adeyemi ta kara da cewa an girke tawagar 'yan sanda masu sintiri domin ci gaba da sa ido da tabbatar da tsaron mazauna yankin.

Kara karanta wannan

N70,000: Kalubale 5 da ke gaban 'yan kwadago da ma'aikata bayan karin albashi

An bazama neman miyagun 'yan bindigan

Ta ce yanzu haka rundunar ta fara bincike kan lamarin kuma an baza jami'ai domin ganin wadanda suka aikata laifin ba su tsira ba.

DSP Ejire-Adeyemi ta kara da cewa:

"Kwamishinan 'yan sanda, Victor Olaiya, ya yabawa jarumta da hanzarin ɗaukar matakin da tawagar sintiri da 'yan bangar VGN suka yi."

Mata 5 sun tsere daga hannun 'yan bindiga

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa mata biyar ciki har da mai goyo suka kubce daga hannun 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Miyagun 'yan bindigan sun kai farmaki garin Dan Isah ne da ke karamar hukumar Kauran Namoda inda suka yi awon gaba da mutane 150.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.