Bayan Dikko Radda, Wani Gwamnan PDP Ya Mika Mulki a gMataimakinsa, Ya Tafi Hutu
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya mika ragamar mulkin jiharsa ga mataimakinsa, Barista Bayo Lawal na tsawon wata guda
- Kakakin majalisar jihar, Adebo Ogundoyin ne ya karanta sakon gwamnan a zauren majalisar yayin zaman majalisar na ranar Alhamis
- Gwamna Makinde ya ce zai tafi hutu daga ranar 5 ga watan Agusta zuwa 6 ga watan Satumba yayin da zai kama aiki washe gari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana aniyarsa ta tafiya hutu daga ranar Litinin 5 ga watan Agusta, 2024 zuwa Juma'a 6 ga Satumba, 2024.
Kakakin majalisar jihar, Adebo Ogundoyin ne ya karanta sakon gwamnan a zauren majalisar yayin zaman majalisar na ranar Alhamis.
Gwamna zai tafi hutu, ya mika mulki
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Makinde ya kuma mika mulki ga mataimakinsa, Bayo Lawal domin ya zama mukaddashin gwamna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi wa wasikar take da: “Hutun shekara-shekara daga 5 ga Agusta 2024 zuwa Juma’a 6 ga Satumba 2024 bisa ga sashe na 190 karamin sashe na 1 na kudin tsarkin mulkin Najeriya."
Sanarwar ta ce:
"Ina sanar da ku cewa, har zuwa kammala hutu na, mataimakin gwamna, Barista Bayo Lawal zai zama gwamna mai rikon kwarya zuwa ranar 7 ga Satumbar 2024."
Dabi'ar Makinde ta mika mulki ga Lawal
Gwamna Makinde ya yi alkawarin dawowa daga hutu a ranar Asabar, Satumba 7, 2024.
Makinde dai ya saba mika mulki ga mataimakinsa duk shekara idan zai tafi hutu, kuma mafi akasari ya fi daukar hutun ne a farkon Agusta ya gama a farkon Satumba.
Dikko Radda ya mika mulki ga mataimakinsa
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya mika mulki ga mataimakinsa, Faluk Lawal Jobe domin tafiya hutu.
Gwamna Radda ya miƙa masa mulkin ne domin tafiya hutun wata ɗaya wanda zai fara daga ranar Alhamis, 18 ga watan Yulin 2024 bayan sanar da majalisa.
An ce wannan ne karo na biyu a tarihin mulkin siyasa a jihar Katsina da wani gwamna mai ci ke neman amincewar majalisa domin miƙa mulki ga mataimakinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng