Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Fadi Lokacin da Za a Rabawa Matasa Tallafin Naira Biliyan 110

Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Fadi Lokacin da Za a Rabawa Matasa Tallafin Naira Biliyan 110

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta ce matasa su kwantar da hankula domin nan gaba kadan za a bude shirin tallafawa matasa na YIF
  • A shirin YIF, matasa za su samu tallafin Naira biliyan 110 domin bunkasa sana'o'insu da kuma fitar da su daga cikin matsin tattali
  • Ministar ci gaban matasa, Dakta Jamila Bio Ibrahim ce ta bayyana hakan yayin ganawa da kungiyar matasan MBYC a birnin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministar ci gaban matsa, Dakta Jamila Bio Ibrahim ta ce nan da wasu 'yan kwanaki masu zuwa za a bude shafin neman tallafin YIF.

Shirin YIF an kaddamar da shi ne da nufin tallafawa matasa da jarin Naira biliyan 100 domin inganta sana'o'i da kuma tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kungiyar matasan Najeriya ta tura sako zuwa ga rassanta 104

Dr. Jamila Bio Ibrahim ta yi magana kan shirin tallafawa matasa da jarin N110bn
Ministar ci gaban matasa ta ce nan gaba kadan matasa za su samu tallafin N110bn. Hoto: @AladiYusuf
Asali: Twitter

Tinubu zai ba matsala tallafin N110bn

Dakta Jamila ta jaddada cewa tallafin kudin zai zama wata kariya ga matasan da ke fuskantar matsalar kudi a kasuwancin su, inji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar ta bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar ban girma da kungiyar matasa ta MBYC ta kai ofishinta da ke birnin tarayya Abuja.

Omolara Esan, Daraktan yada labaran ma'aikatar ya bayyana cewa ministar ta ce asusun YIF yana da niyyar bayar da tallafin kudi, karin ilimi, da kayan aiki ga matasa.

Ga matasan da suka samu tallafin, Dakta Jamila ta ce tana da yakinin za su fita daga cikin matsin tattalin arziki ta hanyar bunkasar kasuwancin su.

Wasu ayyukan gwamnatin Tinubu a shekara 1

A cikin shekara daya na gwamnatin Bola Tinubu, ministar ta ce an samu nasarori da dama, ciki har da amincewa da ba matasa kaso 30 na mukaman gwamnati.

Kara karanta wannan

"Ka tsayar da komai tukun": Sheikh Guruntum ya ja hankalin Tinubu kan halin kunci

Haka zalika ministar ta ce gwamnatin Tinubu ta kara mafi karancin albashi zuwa N70,000, bullo da motocin bas na CNG, saye da rarraba kayan abinci ga talakawan kasar.

Baya ga wanna, Dakta Jamila ta ce akwai shirin dawo da aikin haka da tace mai a cikin gida domin rage farashin mai, da kuma gyara tare da kaddamar da tashoshin jiragen ruwa na Abuja.

Za a fara ba matasan Najeriya alawus

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Tarayya ta shirya biyan matasan da da ba su da aikin yi alawus duk wata a Najeriya.

Ministan kudade a Najeriya, Wale Edun ya ce shirin zai taimakawa matasan ne da ke da kwalin digiri ko na kwalejin ilimi don tsame su daga kunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.