Nollywood: Kungiyar MURIC Ta Fusata da Sabon Fim da Aka Nemi Bata Hijabi da Musulunci

Nollywood: Kungiyar MURIC Ta Fusata da Sabon Fim da Aka Nemi Bata Hijabi da Musulunci

  • Wata kungiya mai kare hakkin musulmi (MURIC) ta gargadi hukumomi a kan wani sabon fim din Nollywood da ake shirin saki
  • Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya ce fitar da fim din da ke nuna mata da shigar musulmi rike da makamai ba daidai ba ne
  • Farfesa Ishaq Akintola ya kara da cewa fim din zai jefa tsanar mata masu sanya hijabi a zukatan al'umma, wanda hakan rashin adalci ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas - Wata kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta yi gargadi a kan wani sabon fim da ke nuna mata a cikin hijabi su na fashi da makami a wani banki.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta yi ram da mai dalilin auren bogi da zargin aikata danyen aiki

MURIC ta bayyana cewa nuna mata da cikakkiyar shigar kamala ta musulunci su na mugun aiki batawa mata musulmi suna ne a cikin jama'a.

Nancy
MURIC ta yi tir da sabon fim din Nollywood Hoto: @nancyisimeofficial
Asali: Instagram

MURIC ta wallafa a shafinta na intanet cewa bai kamata a bari a saki fim din da a yanzu aka fara tallansa a wurare daban daban ba duba ga rashin dacewar haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MURIC ta nemi binciken fim din Nollywood

Kungiyar kare hakkin musulmi ta kasa (MURIC) ta shawarci hukumar tace fina-finai ta kasa (NFVCB) da ta fara binciken sabon fim din Nollywood da ke nuna mata cikin shigar musulmi na aikata mugun aiki.

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana fushinsu, inda ya ce nuna shigar musulunci cikin mummunan aiki, bata suna ne.

Ya ce irin wannan zai sa jama'a su rika yi wa mata musulmi mugun kallo da kuma nuna masu kyama a cikin jama'a, Jaridar Leadership ta wallafa wannan.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Yan sanda sun dakume kwararren barawo ya na tsakiyar sata a Kaduna

MURIC ta ce za a tsige sarkin musulmi

A baya mun ruwaito cewa kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta yi gargadin cewa gwamnatin jihar Sokoto na shirin tsige sarkin musulmi, Sa'ad Abubakar III.

Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana haka, inda ya ce ana shirin ragewa fadar Sarkin musulmi karfi wurin gudanar da sarauta da taba muhibbarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.