Kano: Kotu Ta Umarci Sallamar Muhuyi Rimingado Daga Mukaminsa Nan Take

Kano: Kotu Ta Umarci Sallamar Muhuyi Rimingado Daga Mukaminsa Nan Take

  • Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yi zama kan tuhume-tuhume da ke kan Muhuyi Magaji Rimingado
  • Kotun ta umarci sallamar shugaban yaki da cin hanci a Kano saboda saba umarnin kotu da ya yi bayan kararsa da aka kai
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a, Simon Amobeda shi ya ba da wannan umarni bayan shigar da korafi kan Rimingado a kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano ta umarci sallamar shugaban hukumar yaki da cin hanci (PCACC) a jihar, Muhuyi Magaji Rimingado.

Kotun ta dauki matakin ne saboda saba umarnin kotu da Muhuyi Magaji Rimingado ya yi bayan wasu mutane biyu sun shigar da korafi kansa.

Kara karanta wannan

Akpabio ya yi kuskure, akwai ma'aikatan da ba za su samu albashin N70,000 ba

Kotu ta yi zama game da korafi kan Muhuyi Rimingado
Babbar Kotun Tarayya ta umarci korar Muhuyi Rimingado daga shugabancin hukumar yaki da cin hanci. Hoto: Barr. Muhuyi Magaji Rimingado.
Asali: Facebook

Kano: Kotu ta dauki mataki kan Rimingado

Alkalin kotun, Mai Shari'a, Simon Amobeda shi ya yanke hukuncin kan tuhume-tuhume da ake yi kan Rimingado, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai tun kafin yanke hukuncin, Amobeda ya mika Rimingado ga kwamtin ladabtarwa na lauyoyi domin bincike kan saba dokokin kotu.

Wannan ya biyo bayan shigar da korafi da Mustapha da Muhammad Garo suka yi kan abin da ya shafi hakkinsu na 'yan Adam, Tribune ta tattaro.

Sauran wadanda ake karar bayan Rimingado su ne kwamishinan shari'a a Kano da Babban Sifetan 'yan sanda da wasu mutane uku.

Rimingado ya koma ofis bayan hukuncin kotu

Wannan na zuwa ne yayin da kotun CCT ta dakatar da Rimingado a matsayin shugaban hukumar amma ya ci gaba gudanar da ayyukansa a matsayin shugabanta.

Kara karanta wannan

An samu matsala a zaman Kotu kan shari'ar da Kwankwaso ya shigar da hukumar EFCC

Daga bisani Mai Sahri'a Amobeda ya umarci dakatar da Rimingado daga bincike da kamawa da kuma cin zarafin wadanda ke korafin.

Kotu ta dauki mataki kan Muhuyi Rimingado

A baya, mun kawo muku cewa Kotun da'ar ma'aikata (CCT) ta dakatar da shugaban hukumar yaki da rashawa (PCACC) na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.

Kotun ta dakatar da Rimingado ne biyo bayan zarginsa da ake yi da aikata laifuffuka da suka shafi karbar cin hanci da karya dokar aikin gwamnati.

An tuhumar shugaban hukumar PCACC da boye gaskiya yayin bayyana kadarar da ya mallaka a rayuwarsa da kuma karbar cin hanci da rashawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.