Bayan Tinubu Ya Fara Yaki da Tsadar Rayuwa, an Fitar da Rahoton Tashin Farashin Abinci a Najeriya
- Cibiyar kididdiga ta NBS ta fitar da rahoto game da jihohin da aka fi samun tsadar kayan abinci a fadin Najeriya
- Rahoton da cibiyar NBS ta fitar ya shafi farashin kayayyaki da ake amfani da su na yau da kullum ne a watan Yuni
- Legit ta tattauna da wani mai harkar kayan na'ura mai kwakalwa , Aliyu Jibir Waziri domin jin yadda tashin farashi ya shafe su.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Cibiyar kididdiga ta NBS ta fitar da rahoto kan farashin kayan masarufi a dukkan jihohin Najeriya.
Rahoton da cibiyar ta fitar ya shafi watan Yuni ne bayan Bola Tinubu ya fara daukan matakin rage tsadar abinci a watan da muke ciki.
Jaridar Punch ta wallafa cewa rahoton ya shafi farashin kayan abinci bisa lura da jihohi da yankunan Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda farashin abinci ya tashi a Yuni
Cibiyar NBS ta ce an samu tashin farashin wake, shinkafa, tumatur, garin kwaki, doya a cikin watan Yunin da ya wuce.
Jaridar Tribune ta wallafa cewa NBS ta ce farashin tumatur ya tashi da kashi 55.67% idan aka kwatanta da watan Mayun da ya wuce.
Tashin farashin abinci a jihohi
NBS ta bayyana cewa Abuja aka fi tsadar tumatur, sai kuma jihar Legas ta yi fice a tsadar doya inda jihar Gombe ta yi fice a tsadar garin kwaki.
Haka zalika NBS ta bayyana cewa a jihar Taraba aka fi samun sauƙin garin kwaki yayin da aka fi samun sauƙin farashin doya a jihar Kebbi.
Tashin farashin abinci a yankuna
Kididdigar ta nuna cewa an fi samun tsadar farashin wake a yankin Arewa ta tsakiya yayin aka fi samun tsadar tumatur a Kudu maso gabas da maso yamma.
Yankin Arewa ta yamma ya fi samun sauƙin farashin tumatur haka zalika yankin ya fi samun sauƙin farashin doya.
Legit ta tattauna da Aliyu Jibir Waziri
Wani mai harkar na'ura mai kwakwalwa a jihar Gombe, Aliyu Jibir Waziri ya bayyanawa Legit cewa suma tashin farashi ya shafi harkokinsu.
Aliyu Jibir ya tabbatar wa Legit cewa kaya sun yi matukar tashi ta yadda abin N100,000 yana neman kaiwa N300,000.
Tsadar abinci: Basarake ya yi magana
A wani rahoton, kun ji cewa al'ummar Najeriya na cigaba da kokawa kan yadda kayan masarufi suke kara tashin gauron zabi a kusan dukkan kasuwannin kasar.
Mai martaba sarkin Damaturu, Dakta Shehu Hashimi ibn Umar El-Kanemi ya fara ƙoƙari kan ganin al'umma sun samu sauki a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng