Kudin Wutar Lantarki: Majalisar Wakilai Ta Yi Abu 1 da Zai Kawo Sauƙi Ga Ƴan Najeriya

Kudin Wutar Lantarki: Majalisar Wakilai Ta Yi Abu 1 da Zai Kawo Sauƙi Ga Ƴan Najeriya

  • Majalisar wakilai ta umarci NERC da 'yan kasuwar wutar lantarki da su janye karin kudin wuta da suka yi wa 'yan 'Band A'
  • Majalisar ta bada umarnin ne bayan samun shawarwari daga kwamitinta wanda ya buƙaci a dakatar da ƙarin kudin wutar
  • A watan Afirilu ne 'yan kasuwar wutar lantarkin suka ƙara farashin wutar ga kwastomomin da ke sahun Band A

Abuja - Majalisar wakilai ta umarci hukumar NERC da 'yan kasuwar wutar lantarki (DISCOs) da su janye sabon farashin da suka ƙaƙabawa kwastomomin Band A.

Wannan na zuwa ne bayan shawarar da kwamitin majalisar kan wutar lantarki wanda ya samu jagorancin Benjamin Kalu ya gabatar.

Majalisar wakilai ta yi magana kan kudin wutar lantarki
Majalisar wakilai ta bukaci gwamnati ta janye karin kudin wutar lantarki. Hoto: News24, PropertyPro
Asali: UGC

Majalisar ta karbi dukkanin shawarwarin da kwamitin ya gabatar yayin da ta ce za ta cigaba da bincike kan ƙarin kudin wutar, jaridar Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana zargin an rabawa 'yan majalisa cin hancin N400m domin amincewa da bukatar Tinubu

A watan Afrilu ne muka ruwaito cewa hukumar NERC ta ƙara farashin kudin wutar lantarki amma ga abokan huldar da ke Band A.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta nemi janye karin kudin wuta

A lokacin, an mayar da kudin wutar zuwa N225 kan duk kilowatt ɗaya kuma an yi musu alkawarin samun wutan awanni 20 a rana.

Jaridar Leadership ta ruwaito kwamitin majalisar ya ba da shawarar cewa:

“Kuma a cikin kwanaki 60, su bi tanadin sashe na 116 (2d), (3b), na wannan dokar. Sannan kwamitocin haɗin guiwa su tuntubi ƙwararru domin kayyade nawa ya dace ya zama kudin wutar lantarkin.
"Dukkanin 'yan kasuwa masu rarraba wutar lantarkin su koma tsohon farashinsu na baya har zuwa lokacin da majalisar za ta shawo kan matsalar.
“A ƙarshe, kwamitocin haɗin guiwar sun ce ƙarin farashin wutar lantarki ya zama lokaci zuwa lokaci ne, ya kasance kashi-kashi ba wai kamar yadda suka yi ba."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa, bayanai sun fito

NLC ta magantu kan karin kudi wuta

A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa, kungiyar kwadago ta zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da nuna halin ko in kula game da lamurran jama'ar kasar nan.

Kwamared Joe Ajaero ya bayyana ƙarin kudin wutar lantarki da NERC ta yi da nuna alamar girman kai ƙarara da gwamnatin Najeriya ke da shi.

Shugaban NLC ya ce ƙarin farashin wutar lantarkin zai jawowa 'yan kasuwa da yawa karyewa ko kuma su tsallake su bar ƙasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.