Shugaban Kasa Tinubu ya Amince da Kafa Hukumar Cigaban Jihohi Arewacin Najeriya

Shugaban Kasa Tinubu ya Amince da Kafa Hukumar Cigaban Jihohi Arewacin Najeriya

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kan kudurin dokar samar da hukumar raya yankin Arewa maso Yamma
  • Mataimakin shugaban majalisa, Barau Jibrin, wanda shi ne ya bijiro da kudurin ya ce sanya hannu da shugaban ya yi kyakkyawar alama ce
  • Barau Jibrin ya kara da cewa wannan ya nuna yadda shugaban kasa ya damu kwarai da halin da yankin Arewa maso Yamma ke ciki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kudurin dokar kafa hukumar raya yankin Arewa maso yamma (NWDC).

Wannan hukuma ita ce irinta ta uku da aka samar a kasar nan, bayan takwarorinta da su ka hada da ta raya yankin Arewa maso Gabas da ta Neja-Delta.

Kara karanta wannan

Bayan gyaran kananan hukumomi, Tinubu ya dauko canza fasali ga aikin yan sanda

Barau I. Jibrin
Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan kudurin dokar samar da hukumar NWDC Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ina ne hedikwatar NWDC a Arewa?

Sanata Barau, wanda shi ne ya gabatar da kudurin dokar kafa hukumar, ya bayyana farin cikinsa kan yadda shugaba Tinubu amince da kafa ta, Punch ta wallafa.

Mataimakin shugaban majalisar ya ce shugaba Tinubu ya nuna damuwa kan kalubalen da al’ummar yankin Arewa maso Yamma ke fuskanta.

Ya kuma bayyana cewa hedikwatar NWDC za ta kasance a jihar Kano, inda daga nan ne za ta rika ayyukanta na raya yankin baki daya.

Jihohin Arewan da NWDC za ta yi aiki

Mataimakin shugaban majalisa ya ce hukumar raya Arewa maso Yamma za ta mayar da hankali kan halin da jihohi bakwai da ke yankin ke fuskanta.

Kara karanta wannan

A karon farko, Shugaba Tinubu ya yi magana kan matasa masu shirin yi masa zanga zanga

Jibrin ya ce idan ayyukan NWDC su ka kankama, za ta fuskanci matsalolin da su ka addabi jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara domin magance su.

Majalisa ta amince da kudurin kafa NWDC

A baya mun kawo labarin cewa majalisar dattawa ta zartar da kudurin kafa hukumar raya yankin Arewa maso Yamma bayan an gabatar da rahoto a kanta.

Mataimakin shugaban majalisar, Jibrin Barau daga Kano ne ya gabatar da kudurin, inda ya kuma ji dadin yadda rahoto a kan samar da hukumar ya wakana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.