An Shiga Fargaba a Kano, Cuta Na Neman Hallaka Ƙananan Yara
- Masana sun koka kan yadda cutar tarin fuka ta yawaita cikin ƙananan yara a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya
- Kungiyar kula da lafiya ta SFH ta bayyana yadda cutar ke yawan karuwa a tsakanin ƙananan yara da ke jihar Kano
- Legit ta tattauna da likita, Dakta Zainab Rabi'u Abubakar domin sanin alamar da mutum zai gane yana da tarin fuka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Kungiyar kula da lafiya ta SFH ta yi taro na musamman kan ciwon tarin fuka a jihar Kano.
Masana lafiya sun tattauna kan yadda tarin fuka ya yawaita tsakanin yara ƙanana a fadin jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar SFH ta bayyana kalubalen da ake fuskanta a jihar kan cutar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yawaitar tarin fuka tsakanin yara a Kano
Kungiyar ta bayyana cewa ana samun yaɗuwar cutar tarin fuka a tsakanin yara ƙanana da kashi 5%.
Hakan na nuni da cewa duk cikin yara ƙanana 100 a jihar ana samun yara biyar da ke dauke da cutar.
Wani ma'aikacin jinya, Dakta Ibrahim Umar ya bayyana cewa jihar Kano ce gaba gaba wajen samun masu tarin fuka a Najeriya.
Kalubalen tarin fuka a jihar Kano
Wata ma'aikaciyar lafiya mai suna, Jane Adizue ta bayyana cewa ana fuskantar kalubale da dama dangane da tarin fuka a Kano.
Jane Adizue ta ce akwai kalubalen rashin gwaji da wuri, rashin samun kulawa da rashin bayyana yadda mai cutar ya kamata ya rayu.
Tarin fuka: An yi kira ga gwamnati
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano kan kara kokari wajen wayar da kan al'umma da ɗaukan sauran matakan yaki da cutar.
Dakta Ibrahim Umar ya ce duk da jihar ta samar da kayan gwaji kyauta amma ya kamata a kara kokari kasancewar Kano na da yawan al'umma.
Legit ta tattauna da likita
Wata likita, Dakta Zainab Rabi'u Abubakar ta bayyanawa Legit cewa alamun tarin fuka ba su cika bayyana da wuri ba.
Dakta Zainab ta bayyana cewa daga cikin alamun akwai yin zufa da dare, yawan tari mai hade da jini, ciwon kirji da rashin sha'awar abinci.
Har ila yau, likitar ta shawarci duk wanda yaga daya daga cikin alamun ya gaggauta zuwa asibiti domin gwaji saboda ana iya warkewa daga ciwon.
Gwamnatin Kano za ta yi rusau
A wani rahoton, kun ji cewa yan kasuwa a jihar Kano da ke kan titin Jami'ar Bayero sun yi korafi kan kokarin ruguza musu wuraren sana'a.
Wani dan kasuwa, Ibrahim Mu'azzam ya bayyana halin da suke ƙoƙarin shiga da kuma yin kira ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf kan lamarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng