Najeriya ce kasa mafi yawan masu cutar Tarin fuka a nahiyar Afrika - WHO

Najeriya ce kasa mafi yawan masu cutar Tarin fuka a nahiyar Afrika - WHO

Wakilin kungiyar kiwon lafiya duniya WHO, Tereza Kasaeva, ta alanta cewa Najeriya ce kasa da ta zo na daya a yawan masu fama cutar Tarin fuka a duk fadin nahiyar Afrika.

Hakazalika ta kara da cewa Najeriya na cikin kasashe 10 dake gan gaba da yawam amsu dauke da cutar a fadin duniya.

Kasaeva ta bayyana hakan ne ranar Laraba yayinda ya jagoranci tawagar majalisar dinkin dunya wajen kaiwa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ziyara da ofishinsa dake Abuja.

Ta ce Tarin fuka na hallaka akalla mutane milyan daya da rabi a kowace shekara.

A cewar hadimin shugaban majalisar dattawa,Ezrel Tabiowo, Kasaeva ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta zuba kudi cikin kiwon lafiya cikin gaggawa.

Najeriya ce kasa mafi yawan masu cutar Tarin fuka a nahiyar Afrika - WHO
Najeriya ce kasa mafi yawan masu cutar Tarin fuka a nahiyar Afrika - WHO
Asali: UGC

KU KARANTA Ba wani kokari da gwamnatin Najeriya take yi wajen kawo karshen Boko Haram - Kasar Faransa

Tace, “Akwai bukatar zuba kudi wajen kawar da tarin fuka da sauran cututtuka. Daga bangarenmu, za muyi kokarin kara wayar da kan mutane domin samo kudi na taimakawa kasar.“

“Tsohuwar cuta ce amma itace na daya wajen kisan mutane a duniya saboda mutane milyan daya da rabi ke mutuwa kowace shekara.“

“A nan Najeriya, ku ne na daya a nahiyar Afrika, kuma cikin na goman farko a duniya.“

Shugaban majalisar dattawan ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da kungiyar kiwon lafiyar su taimakawa gwamnatin Najeriya da kudi wajen kawar da cutar tarin fuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel