Rayuka 1.4m za su salwanta, mutane 6.3m za su kamu da tarin fuka saboda dokar kulle a kan cutar korona - Bincike

Rayuka 1.4m za su salwanta, mutane 6.3m za su kamu da tarin fuka saboda dokar kulle a kan cutar korona - Bincike

Wata kungiya mai zaman kanta da ke fafutikar yaki da cutar tarin fuka, ta yi hasashen za a samu karin mutum miliyan 6.3 da za su kamu da cutar a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025.

Kungiyar mai sunan Stop TB Partnership STP, ta kuma ce akalla mutane miliyan 1.4 za su rasa rayukansu sanadiyar cutar ta tarin fuka nan da shekaru biyar din masu zuwa.

Ta ce yiwuwar aukuwar wannan lamari na da nasaba ne da dokar kulle da hana fita da aka shimfida saboda barkewar annobar korona da ta zama ruwan dare a duniya.

STP ta sanar da hakan ne cikin wani rahoto da fitar a ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2020.

Ta ce matakan da aka dauka domin dakile yaduwar cutar korona a duniya, za su haifar da wannan mummunan hatsari na tarin tibi.

Sai dai ta ce an dauki matakan ne cikin rashin tsammani da kuma ba zata na hatsarin yaduwar tarin fuka da duniya za ta tsinci kanta a ciki.

Tana mai cewa, "ana hasashen dokar kulle da kuma rauni da ake fuskanta wajen dakile cutar korona gami da maganinta da ba a samu ba kawo yanzu, za su kara yawan adadin mutanen da za su kamu da cutar tarin fuka da kuma kara yawan adadin rayukan da za a rasa sanadiyar cutar."

An hikaito shugaban kungiyar Dr Lucica Ditiu yana cewa, "sam ba ma daukan izina daga kurakuran baya. A shekaru biyar da suka gabata cutar tarin fuka mai illata kafofin numfashi, ta kasance babbar barazana da ke kashe mutane saboda ba a bata wani muhimmanci."

Yadda cutar tarin fuka ta ke lalata hunhu
Yadda cutar tarin fuka ta ke lalata hunhu
Asali: Depositphotos

"A yau gwamnatoci sun afka cikin mummunan bala'i, suna dabdala a tsakanin annobar korona da kuma annobar tarin fuka wadda likafarta ta dade tana ci gaba.

"Amma sun zabi yin watsi da cutar tarin fuka wadda cikin kankanin lokaci za ta iya rusa duk wani ci gaba da aka gina tsawon shekaru aru-aru."

KARANTA KUMA: Ku daina zarginmu a kan cutar korona - China ta nuna wa Amurka yatsa

"Sun mayar da hankali kan annobar korona wadda ta ke yaduwa tamkar wutar daji da a yanzu ta kwantar da miliyoyin mutane a fadin duniya."

Bayan samun tallafin Hukumar raya kasashe ta Amurka USAID, kungiyar ta gudanar da wannan bincike tare da hadin gwiwar kwalejin Imperial ta kasar Ingila, cibiyar lafiya ta Avenir da kuma Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka.

Binciken ya mayar da hankali kan wasu kasashe mafi girman hatsarin bazuwar cutar tarin fuka wadda tasirin cutar korona zai haddasa. Kasashen sun hadar da Indiya, Kenya da kuma Ukraine.

Kungiyar ta tuna cewa, a shekarar 2018 yayin babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan cutar tarin fuka, shugabannin kasashe da gwamnatoci sun kuduri aniyar daukar mataki na gaggawa akan cutar.

Ta kara da cewa, "a halin yanzu an manta da wannan cutar mai illata kafofin numfashi wadda har a yanzu tana kashe mutum miliyan 1.5 duk shekara a fadin duniya."

"Musibar cutar tarin fuka ta fi ta duk wata cuta mai yaduwa a yanzu."

"Domin dakile mummunan tasirin da annobar korona za ta yi a kan cutar tarin fuka, akwai bukatar gwamnatoci da shugabannin kasashen duniya su ta shi tsaye domin tabbatar da kudirin Majalisar Dinkin Duniya da ta nemi a tashi a farga kan cutar tarin fuka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel