Shin da Gaske An Aikawa Malamai N16m Domin Hana Matasa Zanga Zanga a Arewa?

Shin da Gaske An Aikawa Malamai N16m Domin Hana Matasa Zanga Zanga a Arewa?

Abuja - A tsakiyar watan Yulin nan aka rika jin jita-jita na yawo cewa ana amfani da malamai wajen hana shirya zanga-zanga.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Wasu sun yi ni nisa har su na cewa sai da aka ba wasu manyan malamai Naira miliyan 16 domin su rufewa talaka baki a Arewa.

Legit ta binciki gaskiyar irin wadannan labarai da ake yawo da su a zauren sada zumunta.

Shugaba Bola Tinubu
Zanga-zanga: Ana zargin Shugaba Bola Tinubu ya rabawa malamai kudi Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Zanga-zanga: Ikirarin rabawa malamai N16m

Akwai wani fitaccen mai wasan barkwanci da ya jawo wannan zargi inda a shafin Facebook ya nuna an aikawa duk malami N16m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga baya an ga hotuna na yawo a Facebook da ikirarin an tura N16m ga babban malamin nan, Sheikh Sani Yahaya Jingir.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Malamin musulunci ya yi wa gwamnati da matasa bulaliya a huduba

Kamar yadda hoton ya nuna, an turawa shugaban kungiyar ta Izala ta reshen Jos kudin ne ta asusun wani fitaccen banki a kasar.

Legit Hausa ta bincika ta manhajojin bankuna, amma ba ta iya gano kwakkwarar hujjar da za ta gaskata wannan zargi da ake yi ba.

Da mu ka duba lambar asusun bankin da ake yawo da shi, bai tabbatar da cewa Sani Yahaya Jingir ne ya mallaki akawun din ba.

Menene ya kai malamai zuwa Abuja?

A wani faifen bidiyo, Sheikh Mansur Sokoto ya tabbatar da malamai har 130 sun je Abuja kuma fadawa gwamnati gaskiya ne ya kai su.

Ba zargin karbar N16m ba, Mansur Sokoto ya ce ko N16tr aka ba da ba zai saida al'ummarsa ba.

Daga cikin abubuwan da aka tattauna a cewar Farfesa Sokoto shi ne kokawa kan kuncin rayuwa da nuna adawa ga yarjejeniyar SAMOA.

Dr. Aliyu Muhammad Sani wanda malamin musulunci ne da ke garin Bauchi ya tabbatar da wannan kafin nan a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun soki Ministan Buhari kan goyon bayan zanga zanga

Babu gaskiya a zancen ba malamai kudi

Bayan haka, Legit ta rahoto Farfesa Sa’eed Muhammad Yunusa ya ce sun bincika domin jin gaskiyar ko an ba malamai miliyoyin kudi.

Limamin ya ce a karshe sun gano babu kanshin gaskiya a zargin kuma ya ce za su gayyato malaman domin su fayyace komai a wajen lacca.

Wannan ya zo daidai da maganar malamin musuluncin nan, Barista Ishaq Adam Ishaq kuma babu wata hujja mai nuna akasin haka a yanzu.

Huduba a kan hadarin yin zanga-zanga

Ana da labari Farfesa Sa’eed Muhammad Yunusa ya yi kira ga matasa da shugabanni a lokacin da matasa su ke Shirin zanga-zanga.

Shehin ya ba da misali da abin da ya faru kasashen Sudan, Libya da Siriya don haka ya bukaci a yi hattara kafin lamarin ya kara cabewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng