Shehin Malami ya Musanta Karbar N16m daga Tinubu, ya Fadi Dalilin Ziyartar Shugaban Kasa
- Malaman addinin musulunci na ta karin bayani kan batun zanga-zanga da matasan kasar nan ke shirin gudanar wa
- Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya ce zagin malamai da ake yi ana zaton sun karbo na goro daga shugaba Bola Tinubu kuskure ne
- Malamin ya ce babu malamin da aka zauna da shi a kan batun zanga zanga ballantana a yi maganar karbar toshiyar baki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Najeriya - Shehin malami, Barista Ishaq Adam Ishaq ya musanta labarin cewa malamai sun karbi kudi har Naira Miliyan 16 daga shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A wani bidiyon malamin, an jiyo shi ya na cewa babu yadda za a yi shugaban kasa da ya rika tura wa wani kudi kai tsaye kamar yadda ake yayata wa.
Sheikh Ishaq Adam Ishaq ta cikin bidiyon da @el_uthmaan ya wallafa, ya ce zalunci ne a rika danganta malamai, ciki har da na ahlus sunnah da karbar kudi ana zaginsu a gari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gaskiya kan zaman malamai da Tinubu
Shiekh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana cewa malamai sun ziyarci fadar shugaban kasa ne domin tattaunawa a kan batun yarjejeniyar SAMOA.
Malamin ya ce sun bukaci shugaban kasa da a tabbata Najeriya ta fita daga wannan yarjejeniya saboda illarta ga jama'a, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce rashin adalci ne a rika yada labarin karya ana cewa sun zauna ne domin karbar kudi saboda su yi fatawar haramta zanga-zanga a Najeriya.
"Tsoronmu kan zanga zanga," Sheikh Ishaq
Malamin addinin musulunci, Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana fargabar da su ke da shi a kan zanga-zangar da matasan kasar nan ke shirin gudanarwa.
Malamin ya ce a duba kasashen da su ka yi makamanciyar zanga-zangar a da, da halin da su ke ciki a yanzu, kamar yadda ya buga misali da Libya, Sudan da Syria.
"Lallai masu tsarin zanga-zangar nan su sani, ba wai malamai sun ce zanga-zanga haramun ce saboda son zuciya ba.."
- Shiekh Ishaq Adam Ishaq
Zanga zanga: Sheikh Maqari ya fadi matsayarsa
A baya kun ji cewa shehin malamin nan, Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana matsayarsa a kan zanga-zangar da matasa ke shirin gudanar wa.
Malamin ya ce duk da ba za a haramta zanga-zanga da sunan addinin musulunci ba, amma matasan kasar nan ba su shirya yin ta ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng