Bello Turji Ya Zargi Matawalle da Goyon Bayan Ta’addanci a Bidiyo, Ya Yi Tonon Silili
- Hatsabibin dan ta'adda a yankin Arewa maso Yamma, Bello Turji ya yi tone-tone kan ayyukan ta'addanci a yankin baki daya
- Bello Turji musamman ya zargi tsohon gwamnan Zamfara kuma Ministan tsaro, Bello Matawalle kan goyon bayan ta'addanci
- Legit Hausa ta tattauna da tsohon kwamishina a jihar Zamfara kan zargin da ake yiwa Bello Matawalle
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Gawurtacen dan bindiga, Bello Turji ya zargi Ministan tsaro, Bello Matawalle da daukar nauyin ta'addanci.
Bello Turji musamman ya kira suna tsohon gwamnan Zamfara da cewa shi ya daurewa ta'addanci gindi wanda ya ki karewa.
Bello Turji ya zargi Matawalle kan ta'addanci
Dan ta'addan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafofin sadarwa wanda @Miniko_jnr ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Turji ya ce yana da hujjoji da zai kare zargin da ya yi na cewa gwamnatin da ta shude ita ta daurewa ta'addanci gindi a jihar.
Ya ce mutane da dama da ke Bauchi ko Kaduna ba za su iya sanin abin da ke faruwa na matsaloli a jihar Zamfara ba.
"Gwamnati tana daurewa ta'addanci gindi, akwai wasu mutane daga Zurmi da Shinkafi da Issah ba za su musanta wannan bidiyo ba."
"Ina mai tabbatarwa Gwamnatin Tarayya idan ba su sani ba, zan kira sunaye da hujjoji, ina bukatar da su binciki ayyukan wadannan mutane, na rantse da Allah gaskiya nake fada."
"Gwamnatin Zamfara da ta shude karkashin mulkin Bello Matawalle ta tatauna da 'yan bindiga amma kuma ita ta kawo cikas kan lamarin."
- Bello Turji
Bello Turji ya kamata gwamnati ta fito ta fadi gaskiya kan abin da yake faruwa domin ta bar zargin wasu kan wannan matsalar.
Kalli cikakken bidiyon Bello Turji a nan:
Legit Hausa ta tattauna da tsohon kwamishina a jihar Zamfara kan zargin da ake yiwa Bello Matawalle.
Hon. Mansur Khalifa ya ce ba burinsu ba ne a ce manyan mutane suna da alaka da ta'adanci har sai idan kotu ta tabbatar da haka.
Mansur ya ce amma idan aka samu zargin ya tabbata to ko gwamna ne da kansa ko manyan jami'an gwamanti dole su fuskanci hukunci.
Ya ce ko da basu shiri da mutum ba za su yi masa fatan alaka da ƴan ta'adda ba saboda ba abu ne mai kyau ba.
Bello Turji ya sako wadanda aka kama
Kun ji cewa Ƙasurgumin dan bindiga, Bello Turji ya sako mutum 20 da aka yi garkuwa da su da ke tsare a yankunan Zamfara ta Arewa da jihar Sokoto.
Daga cikin waɗanda aka sako ɗin akwai matar aure mai shekara 19 wacce aka ɗauke sati ɗaya bayan aurenta, yara ƙananan guda uku, tsaffi guda uku.
Asali: Legit.ng