Malami Ya Kasafta Yadda Karamin Ma’aikaci Zai Karar da Albashin N70, 000 a Abinci a Wata

Malami Ya Kasafta Yadda Karamin Ma’aikaci Zai Karar da Albashin N70, 000 a Abinci a Wata

  • Wasu su na murma gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta amince a rika biyan kowane ma’aikaci akalla N70, 000 a wata
  • Inda gizo ke sakar shi ne, tsadar rayuwa ta jawo kusan duka kudin nan za su tafi ne wajen sayen kayan abinci a kasuwa
  • Da wahala karamin ma’aikacin da yake da iyali ya iya tsira da kudin cin nama ko abin da zai saye magani idan an je asibiti

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gwamnatin tarayya da ‘yan kwadago sun cin ma matsaya a game da karin albashin da za a yi wa ma’aikata a Najeriya.

Bola Ahmed Tinubu ya amince kowane ma’aikaci ya rika karbar albashin akalla N70, 000 saboda halin da aka shiga a yau.

Kara karanta wannan

Shugabar NLC ta bayyana wadanda suka hana Tinubu ya kai karancin albashi N100, 000

Albashin N70, 000
Mafi karancin albashin ma'aikaci na N70, 000 zai tafi a sayen abinci Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kabir Danladi Lawanti malami ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya tofa albarkacin bakinsa a game da wannan karin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da yake bayani a Facebook, Dr. Kabir Danladi Lawanti ya nuna albashin na N70, 000 zai tafi ne wajen sayen kayan abinci.

Yadda albashin N70, 000 zai kare

Malamin da ya saba sharhi a kan al’amuran yau da kullum ya ce tiyoyin shinkafa hudu kurum za su cinye N20, 000 a wata.

Da zarar an hada da kwalin taliya, an cinye fiye da rabin sabon mafi karancin albashin.

Bayan nan kuma ana bukatar irinsu manja, man gyada, gishiri, magi da sauransu wadanda za su ci sama da N20, 000 cikin albashin.

Babu gurbin nama a albashin N70, 000

Idan za a yi cefanen gaske, ana bukatar itace, kayan karin kumallo irinsu burodi ko wake, ba a maganar nama da daddawa a miya.

Kara karanta wannan

Kalamai a kan gwamnatin da suka tsumbula Sanata Ndume cikin ruwan zafi a APC da majalisa

A cikin albashin ne ya kamata ma’aikaci ya tanadi kudin biyan hayar gida, asibiti, kudin makarantar yara da na zuwa asibiti.

"Ka ga ƙaramin ma'aikaci na karɓar 70k ɗin shi sai ya shiga kasuwa; Shinkafa tiya hudu 20k,"
"Taliya kwali daya 18k, manja ta 10k, gishiri 200, maggi 1300, man girki 10k…"
"Sai ya riƙe 10k kuɗin mota na zuwa aiki. Saura kuma rikicin duniya da mai rai ake yi."

- Dr. Kabir Danladi Lawanti

NLC ta amince da albashin N70, 000

Bayan an gama zuwa a dawo na tsawon watanni, ana da labarin gwamnatin tarayya ta kara mafi karancin albashi zuwa N70, 000 a wata.

Shugabar NLC a Legas, Funmi Sessi ta ce sun san Bola Tinubu ya so adadin kudin ya kai kamar N100, 000 amma sai gwamnoni suka hana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng