Tarihi Bai Manta Ba: Nasarori da Matsalolin da Aka Samu Lokutan Zanga Zanga a Baya a Najeriya
- Biyo bayan shiryen shiryen gudanar da zanga zanga a Najeriya, al'umma na bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan lamarin
- Sai dai wannan ba shi ne karon farko da aka gudanar da zanga-zanga a Najeriya ba saboda wasu matsalolin da ake fuskanta
- Matashi Muhammad Ibrahim ya bayyanawa Legit abin da zai fitar da shi zanga zanga a wannan karon da yadda yake ganin lamarin zai kasance
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Al'umma a Najeriya na cigaba da tofa albarkacin baki kan shirin zanga zanga da ake son yi domin tsadar rayuwa.
A shekarun baya, an gudanar da zanga zanga da dama a Najeriya wanda suka haifar da nasarori da ma matsaloli.
A wannan rahoton, Legit ta yi dubi kan yadda zanga zanga ta gudana a baya tare da bayyana nasarori da matsalolin da aka samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga zangar cire tallafin mai a 2012
A watan Janairun shekarar 2012 shugaba Goodluck Jonathan ya sanar da cire tallafin man fetur a Najeriya wanda hakan ya jawo zanga zanga mai zafi, rahoton BBC.
Shugaba Jonathan ya kara kudin litar man fetur daga N67 zuwa N120 wanda zanga zangar ta tilasta masa rage kudin zuwa N97.
Sai dai a bangaren barna a lokacin ba a samu munanan abubuwa na sace sace sosai ba kamar yadda aka samu a zanga zangar baya.
Zanga zangar EndSARS a 2020
A shekarar 2020 matasan Najeriya musamman daga kudu sun gudanar da zanga-zanga mai zafi tare da gabatar da bukatu biyar ga gwamnatin Muhammadu Buhari.
A wani abu da za a iya cewa zanga zangar ta yi fa'ida, shugaba Buhari ya amice da dukkan bukatun ciki har da soke rundunar yan sanda ta SARS.
Matsaloli da aka fuskanta a EndSARS
Sai dai zanga zangar ta bar baya da kura wacce ta jawo kashe kashe, kone kone, sace sace har ma da fasa wuraren ajiye abinci da gidajen al'umma.
A yanzu haka dai kallo ya koma kan yadda zanga zangar da ake shirin yi a Najeriya domin ganin ko za a samu nasara ko akasin haka.
Legit ta tattauna da Muhammad Ibrahim
Wani matashi mai suna Muhammad Ibrahim ya zantawa Legit cewa ba makawa maganar fita zanga zanga wannan karon.
Muhammad Ibrahim ya ce baya tunanin akwai fitina da za ta taso saboda akwai mutane masu hangen nesa da ake sa ran cewa za su jagoranci zang zangar a bana.
Kenya: Kotu ta yi hukunci kan zanga zanga
A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun kasar Kenya ta soke umurnin da yan sandar kasar suka yi na hana matasa zanga zanga a birnin Nairobi.
Alkalin kotun ya umurci sufeton yan sandar kasar Kenya da ya gaggauta yada umurnin kotun ga dukkan jami'ansa domin su kaucewa hana matasan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng