APC: Masu zanga-zanga da sunan #EndSARS su na da boyayyar manufa

APC: Masu zanga-zanga da sunan #EndSARS su na da boyayyar manufa

- Mai Mala Buni ya yi tir da zanga-zangar #EndSARS da ake yi a Jihohi

- Shugaban APC na rikon-kwarya ya ce akwai lauje a cikin nadi a tafiyar

- Gwamnan Yobe ya ce za a iya samun matsala idan jama'a su ka yi sake

Mukaddashin shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Alhaji Mai Mala Buni, ya tsoma baki a kan zanga-zangar #EndSARS da ake ta faman yi.

Mai Mala Buni ya ce zanga-zangar da ake yi ta #EndSARS a jihohin Najeriya, za ta iya kai wa ga barkewar rikici a fadin kasar nan idan aka yi sake.

Gwamnan na Yobe wanda ke rike da jam’iyyar APC a matsayin shugaban rikon-kwarya ya ce akwai wata boyayyar manufa a wannan tafiya.

KU KARANTA: Yanzu nan: Gwamnatin Edo ta maka dokar ta ɓacin sa'a 24

Buni ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi hira da shi dazu a gidan yada labarai na BBC Hausa a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, 2020, a shirin safe.

Zanga-zangar #EndSARS wanda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane a Najeriya ta fara ne da sunan fatali da dakarun da ke yaki da masu fashi da makami.

“Miyagu za su iya amfani da wannan dama su kawo hatsaniya, su rikita kasa, su tada hankalin jama’a.” Mai Mala Buni ya ke fadawa BBC Hausa dazu.

Buni ya kara da cewa: “Zanga-zangar da ake yi har yanzu ya nuna akwai boyayyar manufa, bayan gwamnati ta yi na’am da bukatun masu zanga-zangar.”

KU KARANTA: Sojoji sun yi karin haske a game da shirin Operation Crocodile

APC: Masu zanga-zanga da sunan #EndSARS su na da boyayyar manufa
Mala Buni Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban APC na rikon-kwaryan ya ce akwai wasu mabarnatan da su ke jin tsoron aikin dakarun F-SARS, don haka su ka dage sai da aka rusa jami'an.

A hirar da aka yi, Alhaji Buni ya yi kiran a samu zaman lafiya, “Duka shugabanni su san cewa sai ana cikin zaman lafiya ne za a iya cin ma manufa.”

Dazu nan ku ka ji cewa an baza sojoji zuwa titunan Abuja bayan zanga-zangar #EndSARS ta canza salo daga kiran a yi wa aikin 'dan sanda garambawul.

Bayan nan ne kuma aka ji cewa an kubutar da wasu 'yan gidan yari wajen zanga-zanga a Edo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel