Yanzu yanzu: Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita ta awanni 24

Yanzu yanzu: Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita ta awanni 24

- Sakamakon fasa rumbunan abinci da matasa suka yi a sassan Jihar Adamawa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya sanya dokar hana fita na sa'o'i 24

- Dokar ta fara aiki daga karfe 3:00 na yau Lahadi, 25 ga watan Oktoba

- Gwamnan ya jinjina wa matasan da suka kame kansu a lokacin zanga-zangar EndSARS

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya sanya dokar kulle na sa’o’i 24 a fadin jihar, sakamakon karya doka da oda da aka yi a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.

Fintiri ya kaddamar da dokar kullen ne a wani jawabi na musamman a ranar Lahadi, inda yayi gargadin cewa gwamnati ba za ta nade hannu ta ga wasu mutane na tada zaune tsaye ba a jihar.

KU KARANTA KUMA: Jerin manyan ma'aikatu da ɓata garin Filato suka lalata, ciki har da sakatariyar jihar

Gwamnan ya ce dokar kullen zai fara aiki daga karfe 3:00 na ranar Lahadi. Ya kuma ce rashin dakatar da barnar na iya haddasa Asabar rayuka da dukiyoyin jama’a.

Yanzu yanzu: Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita ta awanni 24
Yanzu yanzu: Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar hana fita ta awanni 24 Hoto: Breaking Times
Asali: UGC

Ya ce: “Ya ku jama’ar kasa yan uwana, ba za mu bari bata gari da wasu miyagu su ci karensu ba babbaka ba alhalin muna fama da matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane, fashin shanu, fashi da makami da rikicin makiyaya da manoma.

“Saboda haka, na kaddamar tare da sanya dokar ta kulle na har sai baba ta gani a fadin jihar, daga karfe 3:00 na ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, 2020.”

KU KARANTA KUMA: Ba zai ƙara komai a tattalin arziƙi ba - Ndume ya magantu kan rage albashin ƴan majalisu

Ya yi gargadin cewa an haramta zirga-zirgan ababen hawa a lokacin kulle, sai wadanda aka ba umurni, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce lamarin tsaron ya biyo bayan ayyukan da wasu bata gari suka yi na fasa rumbun ajiya mallakar gwamnatin jihar sannan suka sace kayan tallafin korona.

Gwamnan ya jinjinawa matasa a jihar kan kin bari ayi amfani da su wajen aikata ta’asa tunda aka fara zanga-zangar EndSARS a wasu yankunan kasar.

Ya ce yayinda gwamnati ke mutunta yancin al’umma na neman gyara, ta bayyana cewa akwai hanyoyin nuna fafutuka cikin wayewa.

A gefe guda, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta bukaci matasa da su janye gangaminsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jam’iyyar ta ce za ta tallafa wa shugaban kasa Muhammdu Buhari wajen aiwatar da bukatun masu zanga-zanga don ganin zaman lafiya da hadin kai ya dawo a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel