Matasa Na Shirye Shiryen Zanga Zanga, Tinubu Zai Taho Arewa Domin Raba Tallafi

Matasa Na Shirye Shiryen Zanga Zanga, Tinubu Zai Taho Arewa Domin Raba Tallafi

  • A yayin da al'umma ke kuka kan matsin rayuwa har ake shirin zanga zanga Bola Tinubu zai zo Arewa domin yin yayyafi ga talakawa
  • Gwamnatin jihar Yobe ta yi bayani kan irin shirye shiryen da ake domin tabbatar da karbar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu lami lafiya
  • Haka zalika rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa dukkan matakan tsaro da ya kamata a dauka domin samar da tsaro sun kammala

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kammala shirye shiryen zuwa ziyarar aiki jihar Yobe.

Ana sa ran cewa Bola Tinubu zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka ne tare da raba kayan tallafi ga al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An fadawa Tinubu sirri 3 domin shawo kan talakan Najeriya cikin sauki

Bola Tinubu
Tinubu zai kai ziyarar aiki jihar Yobe. Hon. Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa jami'an tsaro sun tabbatar da an kammala shirye-shiryen karbar shugaban kasa a Tobe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Bola Tinubu zai je Yobe?

Rahotanni sun nuna cewa a gobe Asabar, 20 ga watan Yuli shugaba Bola Tinubu zai ziyarci jihar Yobe.

Bola Tinubu zai kaddamar da shirin raba tallafin noma ne ciki har da raba kayayyakin gonan miliyoyin Naira.

Gwamnatin ta kammala shirin karbar Tinubu

Shugaban kwamitin karbar Bola Tinubu kuma kwamishinan yada labaran jihar, Abdullahi Bego ya ce sun kammala dukkan shirye shirye.

Haka zalika gwamnatin jihar ta yi kira ga matasa kan nuna halin kirki yayin ziyarar da shugaban kasar zai kawo, rahoton Progressive News.

Jami'an tsaro sun yi tanadin zuwan Tinubu

Kwamishinan yan sandan jihar Yobe, CP Ahmad Garba ya ce an sanya jami'an tsaro a wurare domin tabbatar da lamura sun gudana lafiya.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Hakan ya biyo bayan taron hadin gwiwa da dukkan nau'ukan jami'an tsaron jihar suka yi ne domin karɓar shugaba Bola Tinubu.

Mai Mala Buni ya raba tallafi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya kaddamar da rabon tallafin tsabar kuɗi N50,000 ga marayu aƙalla 1,000.

Wannan ba shi ne karo na farko ba domin gwamnan ya maida shirin tallafin marayu a matsayin wani aiki da gwamnatin ke yi duk shekara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng