Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Wanda Ya Kai Hari Masallaci Ana Asuba

Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Wanda Ya Kai Hari Masallaci Ana Asuba

  • Kotu ta tsayar da ranar da za ta yankewa matashin da ya hallaka masallata a Kano hukunci kan laifuffukan da ya riga ya amsa su
  • Legit Hausa ta ruwaito cewa ana zargin Shafi’u Abubakar da cinna wuta a wani masallaci, wanda ya yi silar ajalin akalla mutum 20
  • An ce kotun ta sanya ranar 1 ga watan Agusta domin yanke hukunci kan tuhuma ta biyu da ta uku da ake yi wa Shafiu Abubakar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki, jihar Kano ta sanya ranar yanke hukunci kan matashin da ya kashe masallata a garin Gezawa.

Kara karanta wannan

'Yan ta’adda sun farmaki tawagar mataimakin gwamna awanni bayan kotu ta maida shi kan mulki

An ce kotun ta sanya ranar 1 ga watan Agusta domin yanke hukunci kan tuhuma ta biyu da ta uku da ake yiwa Shafiu Abubakar, wanda ake zargi da hallaka masallata da dama.

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan matashin da ya kashe masallata a Kano
Kotu za ta yankewa matashin da ya kashe masallata a Kano hukunci a watan Agusta. Hoto: Federal High Court
Asali: UGC

A zaman kotun da aka yi a ranar Alhamis, Shafiu Abubakar ya amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da aikatawa kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiya kan harin masallacin Kano

Legit Hausa ta ruwaito cewa ana zargin Shafi’u Abubakar dan shekara 38 daga kauyen Gadan da ke karamar hukumar Gezawa a jihar Kano da cinna wuta a wani masallaci.

Lamarin ya faru ne a lokacin Sallar Asuba a ranar 15 ga Mayu, inda ake zargin Shafiu cinna wuta a masallacin, lamarin da ya yi silar ajalin sama da mutum 20.

A zaman kotun da ya gabata, lauyan masu gabatar da kara, Barista Salisu Tahir, mai wakiltar gwamnatin Kano, ya bukaci a ba su izinin shigar da sabbin tuhume-tuhume da ke nuna ainihin adadin da sunayen wadanda suka mutu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida Gida ta kinkimo ayyukan biliyoyi domin inganta rayuwar talakan Kano

Matashi ya nemi sassauci daga kotu

Shafi'u Abubakar a halin yanzu yana fuskantar tuhume-tuhume hudu da suka hada da kisan kai, yunkurin kisan kai, haddasa mummunan rauni, da kuma tada zaune tsaye.

Lauyan da ke kare shi, Barista Asiya Muhammad Imam daga majalisar taimakon shari’a ta Najeriya, ta roki a yiwa matashin sassauci, tun da ya amsa laifinsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito alkalin kotun, Malam Halhalatul Huza’i Zakariyya ya sanya ranar 1 ga watan Agusta matsayin ranar yanke hukunci kan tuhuma ta biyu da ta uku.

Abba ya magantu kan harin masallacin Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ziyarci masallatan da aka kona a wani masallaci da ke karamar hukumar Gezawa.

Gwamnan ya ce zai rattaba hannu kan hukuncin kisa idan shi ne kotu za ta yanke wa Shafiu Abubakar, wanda ake zargi da aikata laifin ba tare da jinkiri ba

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.