Tinubu Ya Sanya Labule da Shugabannin Kungiyoyin Kwadago, An Samu Bayanai
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago kan mafi ƙarancin albashin da za a biya ma'aikata
- Ganawar ta su na zuwa ne mako guda bayan sun yi irinta kan batun mafi ƙarancin albashin da aka daɗe ana tattake waje a kansa a ƙasar
- Taron na yau na da niyyar cimma matsaya tsakanin gwamnatin tarayya wacce ta yi tayin biyan N62,000 da ƴan ƙwadago waɗanda suka haƙiƙance sai an biya N250,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago sun shiga tattaunawa a birnin tarayya Abuja.
Shugaban ƙasan na tattaunawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon ne kan batun sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Najeriya.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero da takwaransa na ƙungiyar ma'aikata ta kasa (TUC), Festus Osifo, sun hallara a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu na tattaunawa da ƴan ƙwadago
Taron na ranar Alhamis na daga cikin jerin tattaunawar da ake yi tsakanin shugabannin ƙwadago da Shugaba Tinubu, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Ko a makon da ya gabata Shugaba Tinubu ya gana da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon kan batun mafi karancin albashi.
Shugaban ƙasan ya bayyana cewa ma’aikatan Najeriya sun cancanci a kyautata jin daɗin su, ƙarin albashi, da kuma inganta yanayin aikinsu.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai yanke shawara kan tayin biyan N62,000 da gwamnati da ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu suka yi.
Ƙungiyoyin ƙwadagon dai sun haƙiƙance cewa dole sai gwamnati ta biya N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
Mafi ƙarancin albashin da ake biyan ma'aikata yanzu a ƙasar nan shi ne N30,000.
Tinubu zai sanar da mafi ƙarancin albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na iya sanar da adadin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya yau Alhamis, 18 ga watan Yuli, 2024.
Ana tsammanin za a bayyana sabon albashin ne a lokacin da shugaba Tinubu da ƴan kwadago suka koma teburin tattaunawa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng