PDP Ta Fadi Yadda Za a Dawo da Farashin Abinci da Man Fetur Kamar Lokacin Mulkinta

PDP Ta Fadi Yadda Za a Dawo da Farashin Abinci da Man Fetur Kamar Lokacin Mulkinta

  • Jami'yyar adawa ta PDP ta kammala taron masu ruwa da tsaki da ta shirya na kwana biyu a jihar Enugu da ke kudancin Najeriya
  • PDP ta koka kan yadda al'ummar Najeriya ke fama da tsadar rayuwa da wahala cikin shekarun da APC ta yi a kan mulkin Najeriya
  • A ƙarshen taron, jam'iyyar ta fadi hanyar da za a samu mafita a Najeriya lamura su dawo kamar yadda suke a lokacin mulkin PDP

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - A jiya Laraba ne jami'yyar PDP ta kammala taron masu ruwa da tsaki na kwana biyu a jihar Enugu.

Jam'iyyar ta koka kan yadda lamura ke kara tabarbarewa a mulkin APC a faɗin Najeriya wanda hakan ke mayar da kasar baya.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Gwamnonin PDP
PDP ta koka kan tsananin rayuwa a mulkin APC. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Muhammad.
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin wani sako da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP: 'APC kawo wahalar rayuwa'

A cikin bayanin ƙarshen taro da jam'iyyar PDP ta fitar ta nuna cewa APC ta kawo tsare-tsaren da suka jefa al'umma cikin tasko.

PDP ta ce duk ayyukan cigaba ta da kawo cikin shekaru 16 APC ta lalata su ta jefa mutane cikin talauci da wahalar rayuwa.

PDP: 'Za mu sassauta lamura'

Jam'iyyar PDP ta ce idan aka zabe ta a 2027 za ta dawo da lamura kamar yadda suke a mulkin da ta yi a shekarun baya.

Ta ce za a samu saukin rayuwa, abinci ya yi sauki, farashin mai ya sauko kasa da kuma kara darajar Naira a duniya.

Kiran jam'iyyar PDP ga yan Najeriya

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun buɗe wuta kan matafiya, sun yi awon gaba da mutane da yawa

A karshe, jam'iyyar PDP ta yi kira ga yan Najeriya kan cewa su kara hakuri kuma su nisanci tashin hankali a fadin kasa, rahoton Daily Trust.

PDP ta ce ƙarshen tsananin rayuwa a Najeriya yana cikin samun nasarar ta a 2027 saboda haka mutane su mara mata baya yayin zabe mai zuwa.

Matan jam'iyyar PDP sun yi zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa wasu matan PDP sun gudanar da zazzafan zanga zanga a birnin tarayya Abuja saboda rashin jin dadin wasu lamuran jami'yyar.

Jagorar mata masu zanga zangar, Dakta Obianuju Ogoko ta bayyana matsalolin da suke fuskanta a tafiyar mata a jami'yyar PDP a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng