An Gano Jihohin da Mamakon Ruwa Zai Jawo Gagarumar Ambaliya
- Gwamnatin tarayya ta yi gargadin za a yi ambaliyar ruwa a garuruwan kasar nan 94 cikin kwanaki biyar
- Ministan muhalli, Dr. Iziak Salako ya ce ambaliyar za ta afku a jihohi 22 daga cikin 36 da ake da su a Najeriya
- Dakta Salako ya ce daga cikin jihohi akwai Adamawa, Kano, Jigawa, Yobe, Katsina da Kebbi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi gargadin samun gagarumar ambaliya a jihohin kasar nan 22.
Garuruwa 94 ne ake fargabar ruwa zai shanye saboda mamakon ruwa da za a yi na kwanaki biyar- daga ranar Talata 16 Yuli, 2024 zuwa 20 Yuli, 2024.
A wani rahoto da ya kebanta da Jaridar Punch, Ministan muhalli, Dr. Iziak Salako ya ce akwai fargabar ruwan zai yi barna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohi da yankunan da za ayi ambaliya
Minista Iziak Salako ya ce ruwa kamar da bakin kwarya zai shafi wasu yankuna a jihohi da ke Arewa da Kudancin Najeriya.
Jihohin da yankunan da ake hasashen ambaliya za ta shafa sun hada da;
1. Adamawa - Gbajili, Ganye
2. Abia - Eziama, Arochukwu
3. Anambra - Onitsha
4. Akwa Ibom - Uyo, Upenekang, Oron, Edor, Eket, Obianga, Etinan 5. Bauchi -Tafawa Balewa, Bauchi
6. Bayelsa - Letugbene
7. Borno State Maiduguri
8. Cross River Ikom, Calabar, Itigidi, Akpap
9. Nasarawa - Udeni, Tunga
10. FCT - Abaji, Bwari 11. Jigawa - Miga, Ringim, Dutse, Hadejia
12. Kano - Gezawa, Gwarzo, Kano, Karaye, Wudil, Sumaila
13. Kebbi - Gwandu, Jega, Kangiwa, Gauri-Banza, Ribah, Sakaba, Saminaka, Kamba, Birnin Kebbi, Bunza, Argungu, Bagudo 14.Katsina - Bindawa, Jibia, Kaita, Katsina, Daura, Funtua 15. Kwara - Kosubosu)
16. Niger - Ibi, Bida, Kontagora, Mashegu, Minna, New Bussa, Katcha, Rijau, Wushishi 17. Plateau -Jos, Mangu
18. Rivers - Port-Harcourt, Onne, Okrika, Bori
19. Sokoto - Makira, Goronyo, Isa, Silame, Sokoto, Wamako 20. Taraba - Gembu, Beli, Garkowa, Gasol, Serti, Donga, Duchi, Gwarzo, Gun gun Bodel
21. Yobe -Gashua, Gasma, Damaturu, Geidam, Kanama
22. Zamfara - Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi, Bukkuyum, Majara, Gummi
Ruwa ya yi barna a Yobe
A baya mun ruwaito cewa mamakon ruwan sama a jihar Yobe ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane uku a karamar hukumar Nangere.
Shugaban hukumar bayar da agaji na jihar, Dakta Muhammad Goje da ya tabbatar da lamarin, ya ce ruwan ya lalata gidaje 50.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng