Bayan Shekara 4: Kotu Ta Raba Gardama Kan Buƙatar Cire Larabci Daga Jikin Takardun Naira
- Kotu ta yi watsi da wata karar da wani lauya ya shigar na bukatar cire rubutun larabci daga jikin takardun Naira
- Lauya Malcom Omirhobo ya ƙalubalanci rubutun larabcin da ke jikin Naira ne yana mai cewa cin fuska ne ga tsarin mulki
- Sai dai a hukuncin da ta yanke, kotun ta ce lauyan ya gaza kawo hujjar cewa CBN yana da wata makarkashiya kan rubutun
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Wata babbar kotun tarayya da ke da zama a Legas ta kori karar da aka shigar gabanta na ƙalubalantar rubutun larabci da ke jikin takardun Naira.
Mai shari'a Yellin Bogoro ta ce sashe na 53 (1) na dokar bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi ta BOFIA ta sahalewa CBN tsarawa, bugawa da raba takardun Naira.
Alkaliyar ta ce lallai sai ya kasance akwai wata doka da CBN ya karya wajen tsara kudin kasar ne kotu za ta iya daukar mataki a kai, inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauya ya ƙalubalanci tsarin Naira
Kotun ta yanke hukuncin cewa, Malcom Omirhobo, wanda ya ƙalubalanci saka larabci a takardun Naira, ya gaza ba da hujjar CBN ta karya wata doka.
A watan Janairun 2020 ne Omirhobo, wani lauya a Legas ya shigar da karar CBN gaban kotun inda ya nemi a cire rubutun larabci da ke jikin takardun Naira.
Jaridar The Punch ta ruwaito lauyan ya ce Larabci ba tare bane cikin yaruka hudu da aka amince da su a Najeriya da suka hada da Turanci, Yarabanci, Hausa da Igbo.
Ya yi ikirarin cewa saka labarci a jikin takardun kudin Najeriya cin fuska ne ga kudin tsarin mulki kasantuwar ba yaren kasar bane.
Kotu ta kori bukatar Lauya Omirhobo
A hukuncin da Mai shari'a Bogo ta yanke a yau Talata, ta ce Omirhobo ya gaza kawo hujjar cewa CBN na da wata manufa wajen saka rubutun larabcin.
A na shi martanin, lauyan ya ce har yanzu bai hakura ba, zai dauki mataki na gaba da zarar ya kammala bitar kwafin hukuncin shari'ar da kotun ta yanke.
CBN zai a iya cire larabci a jikin Naira?
A wani labarin, mun ruwaito cewa babban bankin Najeriya CBN ya bayyana cewa ba zai iya cire rubutun larabci daga jikin takardun Naira ba saboda wani ko wata kungiya sun shigar da kara.
CBN ya mayar da martani kan karar da wani lauya ya shigar inda bankin ya ce rubutun ajamin da ke jikin kudin Najeriya ba yana nufin wani addini ko hulda da larabawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng