Abin Da Ya Kamata Kowane Ɗan Najeriya Ya Sani Game Da Harrufan Larabci a Sabbin Takardun Naira

Abin Da Ya Kamata Kowane Ɗan Najeriya Ya Sani Game Da Harrufan Larabci a Sabbin Takardun Naira

Yan Najeriya da dama sun ci gaba da nuna shakku game da sabon takardun naira. A cewar wasu daga cikinsu, rashin cire harrufan Larabci alama ce da ke nuna cewa addinin Islama yana da karfi a kasar tsarin duk da cewa ana daukar ƙasar a matsayin ƙasa mara bin wata addini a hukumance.

Menene harrufan larabci da ke jikin wasu takardun naira?

Don a karin haske, kalmar da ta dace da wannan harrufan Larabci ita ce 'Ajami'. Tsarin rubutu ne na Afirka wanda aka samo daga Larabci. Hausawa suna da Ajami don rubutu cikin harshen Hausa don haka wasu ke zaton larabci ne.

Sabbin takardar naira
Bayani: Abin Da Ya Kamata Kowane Dan Najeriya Ya Sani Game Da Harrufan Larabci a Sabbin Takardun Naira. Hoto: Bashir Ahmad.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Menene Ajami a wurin yan arewa?

Kara karanta wannan

Ghanim Al-Muftah: Abubuwa 8 Masu Jan Hankali Game da Matashin Da Ya Jika Zukatan Jama'a a Bude Wasan WC a Qatar

A cewar The Cable, galibin yan arewa sun iya karanta Ajami ko da yake ba su fahimci harrufan Latin da ake amfani da shi a harshen turanci ba. Yawancin ’yan Arewa sun kware a Ajami, kasancewar sun yi karatun Al-kur'ani tun suna yara.

Hujjar da ke goyon bayan Ajami

Tunda rubutun Ajami yana cikin harshen Hausa kuma ba alama ce ta Musulunci ko wani addini ba, mutane da dama za su iya kafa huja cewa ba a karya doka ba.

Hujjar rashin goyon bayan Ajami

Hujjar rashin goyon bayan rubutun ajami a takardun naira shine ya saba wa sashi na 10 da 55 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya wanda ya ce tarayyar ba za ta zabi wani addini a matsayin addinin kasa ba.

Kallon da aka yi wa Larabci da musulunci a matsayin abu guda, ya janyo zargin cewa harrufan 'Larabci' a takardar naira na nuna addini ko goyon bayan musuluntar da kasa.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Akwai rubutun Ajami a dukkan takardun kudin Najeriya?

Gwamnatin tarayya, a watan Fabrairun 2007, ta cire harrufan larabci a kananan takardun naira. A cewar FG, babu bukatar ajamin domin mafi yawancin yan Najeriya yanzu sun iya karatu da rubutu a harshen turanci.

Kara a kotu

Amma, gwamnatin tarayya da babban bankin kasa, CBN, da antoni-janar na tarayya, AGF, suna fafatawa a kotu da karar da wani lauya mazaunin Legas, Malcolm Omirhobo ya shigar yana neman a cire rubutun ajamin daga naira don suna 'wakiltar musulunci ne'.

Buhari ya bayyana dalilin sauya sabbin takardun naira

Premium Times ta rahoto cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Laraba a Abuja ya kaddamar da sabbin takardun Naira inda ya nuna farin cikinsa kan sake fasalin kudin kasar nan da aka samar a cikin kasar karkashin Nigerian Security Printing and Minting (NSPM) PLC.

A yayin jawabi lokacin kaddamar da takardun nairan, wanda aka dasa kuma da taron majalisar zartarwa na tarayya, Buhari yayin bayanin dalilin da yasa ya amincewa babban bankin kasa sake fasalin N200, N500 da N1,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel