An Cafke Hamshaƙin Ɗan Crypto a Abuja, Ana Zargin Yana Ɗaukar Nauyin Ƴan Ta’adda

An Cafke Hamshaƙin Ɗan Crypto a Abuja, Ana Zargin Yana Ɗaukar Nauyin Ƴan Ta’adda

  • Rundunar 'yan sandan Abuja, ta tabbatar da kama hamshakin biloniyan ɗan crypto, Linus William wanda aka fi sani da Blord
  • Kamar yadda kakakin rundunar ya bayyana, an mika musu korafe-korafe game da Blord tare da kamfanoninsa kan zargin damfara
  • Baya ga zargin ɗan kirifton da damfarar yanar gizo, ana zargin yana daukar nauyin ta'addan da kuma taimakawa 'yan damfara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun kama hamshakin ɗan crypto, Linus William, wanda aka fi sani da Blord.

An kama Blord ne a Abuja a ranar Talata bayan zarginsa da ake yi da damfarar jama'a a harkar crypto, daukar nauyin ta'addanci da taimakawa masu damfara a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Ranar Ashura: An tsananta tsaro a Kaduna, ƴan sanda sun haramta taron ƴan Shi'a

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan kama fitaccen dan crypto a Abuja
'Yan sanda sun kama Blord, fitaccen dan crypto a Najeriya. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, Najeriya ACP Muyiwa Adejobi, ya fitar da sanarwar kama dan crypto din a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ACP Adejobi ya bayyana cewa rundunar ta kama Linus William ne saboda korafe-korafe kan kamfanoninsa ya yi yawa.

'Yan sanda za su binciki dan crypto

Kakakin rundunar 'yan sandan ya yi alkawarin cewa 'yan sanda za su yi bincike ciki da waje kan lamarin.

A cewar sanarwar da Adejobi ya fitar:

"A halin yanzu dai sashen CID na rundunar 'yan sanda (NPF-NCCC) na binciken korafe-korafen da aka shigar a kan rukunin kamfanonin Blord, BLord Real Estate, BLord Jetpaye da Billpoint Technology.
"Laifukan da ake tuhumarsa da su sun hada da damfarar kudin crypto, taimakawa masu damfarar yanar gizo, daukar nauyin ta'addanci da kuma kin kiyaye dokokin kasa.
“Za mu yi binciken da ya dace mai zurfi. Dole ne yanar gizon mu ta kasance mai aminci da tsaro ta kowanne fanni. Mun shirya tabbatar da hakan."

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi luguden wuta kan ƴan ta'adda a Arewa, sun faɗi nasarar da aka samu

An daure dan crypto shekara 11,000

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kotu ta tasa keyar Faruk Fatih Ozer shekaru dubu 11,196 a gidan kaso kan zargin damfara a yanar gizo ta hanyar amfani da kudin crypto.

An daure Faruk wanda shi ne ya kirkiri wani kudin crypto da 'yan uwansa guda biyu kan damfara da kuma kirkirar kamfanin zalunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.