N1555/$1: Naira Ta Ruguzo Ƙasa Yayin da Dala Ta Lula Sama a Kasuwar Hada Hadar Kuɗi
- A yayin da hukumar NBS ta fitar da rahoton cewa hauhawar farashin kayan abinci ya karu, a hannu daya kuma darajar Naira ta karye
- A ranar Litinin, darajar Naira ta fado kasa zuwa N1,555/$1 a kasuwar hada-hadar kudi sabanin N1545/$1 da aka yi cinikinta a makon jiya
- Adadin dalar Amurka da aka yi hada-hadarsu a kasuwar ya karu da kashi 21.3 zuwa dala miliyan 153.53 daga dala miliyan 126.5 a yanzu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A jiya Litinin, 15 ga watan Yulin 2024, darajar Naira ta fado kasa zuwa N1,555/$1 a kasuwar hada-hadar kudi daga N1,545/$1 da aka yi kasuwancinta a Juma'ar makon jiya.
Hakazalika, darajar Naira ta fadi kasa zuwa N1,577.29/$1 a kasuwar canji ta Najeriya mai cin gashin kanta, NAFEM, kamar yadda rahoton kasuwar ya nuna.
Yadda aka yi hada-hadar Naira/Dala
Farashin canjin NAFEM ya tashi zuwa N1,577.29/$1 daga N1,563.8/$1 Juma'ar makon jiya, wanda ke nuna faduwar darajar Naira da N13.49, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adadin dalar Amurka da aka yi hada-hadarsu a kasuwar ya karu da kashi 21.3 zuwa dala miliyan 153.53 daga dala miliyan 126.5 da aka yi ciniki a ranar Juma'a.
Sakamakon haka, tazarar da ke tsakanin kasuwannin bayan fage da farashin NAFEM ya ragu zuwa N18.8 kan kowace dala daga N18.8 kan kowace dala.
Duba wasu labaran akan canjin Naira zuwa Dala:
Naira tayi zuciya, darajar kudin Najeriya ta farfado a kasuwar canji
Darajar Naira ta ƙara sama yayin da Dala ta karye a kasuwar musayar kuɗi a Najeriya
Murna yayin da farashin Dala ya ƙara karyewa a kasuwar hada hadar kudi a Najeriya
Dalar Amurka ta ƙara yin raga-raga da Naira a kasuwar musayar kuɗi a Najeriya
Meyasa Naira ta faɗi ƙasa kan Dala?
A wani labarin, mun ruwaito cewa darajar kuɗin Najeriya watau Naira ta ragu da kaso 23% a watan Afrilun 2024 wanda ba a taba ganin irinsa ba tun watan Fabrairun 2024.
Ƙaruwar neman Dala a kasuwannin bayan fage da bankuna da gazawar bankin CBN wajen ba ƴan canji Dala a kan lokaci, ya jawo darajarta ta faɗi kamar yadda rahoto ya nuna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng