Matsalar Tsaro a Abuja: Ƴan Bindiga Sun Harbi Jigon APC, Sun Tafi da Mutane 5
- Miyagun 'yan bindiga sun kutsa yankin Yangoji dake karamar hukumar Kwali a babban birnin tarayyar Abuja inda suka shiga gida-gida
- An ruwaito cewa, 'yan bindigar sun fasa tagar gidan jigon jam'iyyar APC tare da kutsawa ciki, inda suka harbe shi da kuma ace 'ya'yansa
- 'Yan bindiga sun kuma shiga wurin makwabtansa inda nan ma suka iza keyar wasu mutane uku, abin da aka jima ba a gani ba a yankin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Masu garkuwa da mutane sun sace mutane biyar mazauna yankin Yangoji dake karamar hukumar Kwali a babban birnin tarayyar Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigar sun harbi Alhaji Musa Majaga, wani jigon jam'iyyar APC mai mulki bayan sun shiga har cikin gidansa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin Yangoji wanda ya bayyana sunansa da Malam Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne ranar Litinin wurin karfe 12:23 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kai hari a Abuja
Malam Abdullahi ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun kutsa gidan jigon APC a yankin, bayan lalata tagogin gidan tare da kutsawa har cikin dakinsa.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun lalata tagogin gidan Majaga inda suka shiga har dakinsa tare da harbinsa. An gano cewa, sun yi garkuwa da 'ya'yansa biyu.
Malam Abdullahi ya ce:
"Sun harbe shi kuma sun dauke 'ya'yansa biyu. Bayan nan kuma sun shiga gidan makotansa inda suka yi awon gaba da mutane uku."
'Yan sa-kai a Abuja sun yi korafi
Wani 'dan sa kai, wanda yayi magana da jaridar a ranar Litinin, ya ce 'yan sa kai basu da wasu isassun harsasai da za su iya kai dauki yayin harin 'yan bindigar.
Dan sa-kan da ba a bayyana sunansa ba ya ce:
"Mun fahimci cewa 'yan bindigar na da masaniyar 'yan sa-kan yankin basu da harsasai a bindigoginsu, shi ya sa suka kawo harin kansu tsaye..
"Sun kawo farmakin tare da sace mutane biyar. Ba mu taba fuskantar farmakin 'yan bindiga ba a watanni 5 da suka gabata a nan yankin Yangoji."
'Yan sanda sun nemi karin lokaci
Dan sa-kan ya ce jigon jam'iyyar APC da aka harba a kafarsa yana kwance a wani asibitin kudi dake Gwagwalada domin samun taimakon likitoci.
Kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, SP Adeh Josephine, ta bukaci a ba ta lokaci domin ta binciko abin da ya faru.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba ta dawo da kiran da aka yi mata ba.
'Yan bindiga sun gamu da matsala a Abuja
A wani labari na daban, mun ruwaito cewa miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen dawaki dake babban birnin tarayyar Najeriya.
Sai dai, babu kakkautawa 'yan sanda suka hanzarta kaiwa mazauna yankin dauki inda aka buga gumurzu tsakaninsu da miyagun tare da fatattakarsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng