Yarjejeniyar Najeriya da Kamfanin X: Kotu Za Ta Titsiye Tsohon Ministan Yada Labarai

Yarjejeniyar Najeriya da Kamfanin X: Kotu Za Ta Titsiye Tsohon Ministan Yada Labarai

  • Kotu ta umarci tsohon ministan yada labarai da ya fito da kwafin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin X
  • Kungiyar SERAP ce ta shigar da kara gaban Mai shari'a Nnamdi Okwy Dimgba inda ta nemi duba yarjejeniyar domin gano abin da ta kunsa
  • Nnamdi Okwy Dimgba ya ce fitar da bayanan yarjejeniyar zai sa SERAP ta gano ko an tauye 'yancin 'yan Najeriya a cikin yarjejeniyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta umarci Alhaji Lai Mohammed, tsohon ministan yada labarai da ya bayyana abin da ke cikin yarjejeniyar Najeriya da kamfanin X (Twitter).

Mai shari'a Nnamdi Okwy Dimgba ya yanke hukuncin a watan Mayun 2024 bayan kungiyar SERAP ta shigar da kara mai lamba FHC/L/CS/238/2022 kan lamarin.

Kara karanta wannan

An bayyana wadanda suke son ruguza APC domin yiwa Tinubu illa

Kotu ta yi magana kan yarjejeniyar Najeriya da kamfanin X
Kotu ta umarci Lai Mohammed ya fito da bayanan yarjejeniyar Najeriya da kamfanin X. Hoto: @elonmusk, @BashirAhmaad
Asali: Twitter

SERAP ce ta bayyana hukuncin da kotun ta yanke a shafinta na X a yau Lahadi bayan da ta samu kwafin hukuncin kotun a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta ba ministan Buhari umarni

Kamar yadda bayanin hukuncin da SERAP ta wallafa, Mai shari'a Nnamdi Dimgba ya umarci tsohon ministan yada labaran da ya:

"Mika kwafin yarjejejniyar Najeriya da X (tsohuwar Twitter) ga kungiyar SERAP domin duba ko yarjejeniyar ta sabawa 'yancin 'yan Najeriya."

Mai shari'a Nnamdi Dimgba ya ce bayyana abin da yarjejeniyar ke dauke da shi ba zai shafi 'yancin Twitter ko na tsaron Najeriya ba.

Kotu ta watsi da korafin tsohon ministan

Sanarwar ta kuma ce alkalin kotun ya yi watsi da korafin da lauyan tsohon ministan ya gabatar tare da amincewa da bukatar SERAP, inda ya umarci Lai Mohammed ya mika bayanan.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Malaman Katolika sun ba gwamnatin Tinubu zabi 2 kan yarjejeniyar Samoa

Kotun ta gano cewa tsohon ministan ya gaza kawo hujjar cewa tsohon shugaban kasar ya bi matakan da suka dace wajen ayyana Twitter matsayin babbar kafar yada labaran kasar nan.

Mai shari'a Dimgba ya kuma jaddada cewa lauyan ministan ya gaza gabatar da kwakkwarar hujjar yadda bayyana bayanan yarjejeniyar zai cutar da kasuwancin Twitter.

Duba bayanin hukuncin kotun a kasa:

Twitter ta yi zama da gwamnatin Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin X (tsohuwar Twitter) ya gana da gwamnatin Najeriya domin kulla yarjejeniya bayan da aka dakatar da ayyukan shi a kasar.

Ministan yada labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan, inda ya ce kamfanin na Twitter ya yi rijista da hukumar NBS kuma ya kiyaye dukkanin ka'idojin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.