Twitter ta rubutowa FG wasika, tana bukatar a tattauna kan dakatar da ita
- Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa Twitter ta zo mata da bukatar zama a yi sasanci
- Kamar yadda ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed yace, dama can kofa bude take
- Mohammed yace dole ne Twitter ta yi rijista da NBC kuma ta kiyaye abubuwan da za a dinga wallafawa
Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta tabbatar da cewa Twitter ta rubuto mata wasika da bukatar tattaunawa kan matsalolin da suka sa gwamnatin ta dakatar da ita.
Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya tabbatar da hakan yayin da ya bayyana a shirin "siyasar kasa baki daya", wani shirin gidan rediyon Najeriya ne da Kamfanin Dillancin Labarai ya kiyaye a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.
KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 56 da kifi ya hadiye kuma ya amayo shi, ya bada labari dalla-dalla
"Ina tabbatar muku da cewa Twitter ta yi wa gwamnatin tarayya wasika na cewa ta shirya tattaunawa.
"Kamar yadda muka ce, kofa a bude take amma sai Twitter ta yi abinda ya dace," yace.
Ministan ya jaddada matsayar gwamnati na cewa ba za ta lamuncewa kowacce irin kafar sada zumunta ba da zata taimaka wurin tarwatsa kasar nan.
Mohammed ya ce daga cikin sharuddan dawowar Twitter Najeriya shine dole ne a yi yarjejeniya kan abinda za a iya wallafawa.
Yace Twitter da sauran kafafen sada zumunta dole ne su yi rijista tare da samun lasisi daga NBC kuma su kiyaye sharuddan lasisin tare da biyan haraji, rahoton NNN.
Kamar yadda ministan yace, sanya dokokin kafafen sada zumunta al'ada ce ta kowacce kasa a duniya.
Ya ce kasashe da yawa yanzu sun gano cewa kafafen suna karfi fiye da gwamnati kuma dole ne a saka musu sharuddan.
"Singapore, Algeria, Pakistan, Turkey duk suna da dokokin kiyaye kafafen sada zumunta, Australia haka.
"Hatta EU da bata da wasu dokoki dangane da kafafen sada zumunta ta yi haka a rubuce," yace.
KU KARANTA: Nnamdi Kanu dan ta'adda ne da IPOB yake kasuwanci, Cewar Asari Dokub
A wani labari na daban, Rundunar sojin Najeriya tayi kira ga 'yan ta'addan Boko Haram da su ajiye makamai kuma su nemi yafiya tare da sasanci.
AA Eyitayo, babban kwamandan Div 7 na rundunar sojin kasa, yayi wannan kiran a ranar Lahadi a wani taro da rundunar ta shiryawa manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Eyitayo ya ce 'yan ta'addan Boko Haram suna cikin dimuwa bayan gagarumin luguden wuta tare da matsanta musu da sojoji suka yi, TheCable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng