Dakatar da Twitter: Gwamnati ta ba da alamar yaushe za a dawo yin Twitter

Dakatar da Twitter: Gwamnati ta ba da alamar yaushe za a dawo yin Twitter

- Fadar shugaban kasa ta bayyana dakatar da Twitter da cewa na dan wani lokaci ne ba din-din-din ba

- A wata sanarwa, fadar ta bada alamar cewa za a sake ba 'yan Najeriya damar amfani da kafar nan ba da jimawa ba

- Dakatar da Twitter ya jawo cece-kuce a Najeriya da sauran kasashen duniya, inda aka ta sharhi kan dakatarwar

Fadar shugaban kasa ta bayyana dakatar da Twitter a Najeriya a matsayin na dan wani lokaci, inda ta ba da alamun cewa nan ba da jimawa ba ‘yan Najeriya za su samu samu damar sake shiga kafar ta yanar gizo.

Legit.ng ta lura cewa wannan bayanin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni.

Yayin da yake karin haske kan dalilin da ya sa aka dakatar da Twitter, Shehu ya bayyana matakin gwamnatin a matsayin "na wani lokaci".

KU KARANTA: NCC Ta Ba Kamfanonin Sadarwa Umarnin Hana ’Yan Najeriya Damar Hawa Twitter

Dakatar da Twitter: Gwamnati ta bada alamar yaushe za a dawo yin Twitter
Dakatar da Twitter: Gwamnati ta bada alamar yaushe za a dawo yin Twitter Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A wani bangare na sanarwar, gwamnatin ta ce:

Shehu ya bayyana cewa "an samu matsaloli da dama game da kafar sada zumuntar a Najeriya", ya kara da cewa kamfanin ya gaza magance matsalolin.

Shehu ya bayyana cewa "an samu matsaloli da dama game da kafar sada zumunta a Najeriya", ya kara da cewa kuma kamfanin ya gaza magance matsalolin.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya sanar da dakatar da Twitter a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Juma’a, 4 ga watan Yuni.

Ya bayyana dalilin daukar matakin na gwamnati da zargin ana amfani da dandamalin don ayyukan da za su iya gurgunta ci gaban Najeriya.

Wannan ci gaban ya tunzura 'yan kasa tare da bayyana martani daga kasashen duniya duk da cewa kamfanin Twitter yayi alkawarin yin duk abinda zai iya don ganin 'yan Najeriya sun sake samun damar shiga shafin nasa.

KU KARANTA: Dakatar Da Twitter: Shehu Sani Ya Bayyana Hanya Mafi Sauki Don Hawa Twitter

A wani labarin, Kafafen sada zumunta sun cika da cece-kuce biyo bayan umarnin gwamnatin Buhari na dakatar da ayyukan Twitter a fadin kasar saboda goge rubutun shugaban kasa da Twitter din ta yi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki, sun tofa albarkacin bakinsu kan umarnin na gwamnatin Buhari.

A wasu rubutun da Legit.ng Hausa ta gano na jiga-jigan 'yan siyasan, ta gano inda suke martani kan batun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel