Halal Ko Haram: Jerin Malaman da Suka Goyi Bayan Zanga Zanga da Wadanda Suka Hana
- Kan malaman addinin Musulunci ya rabu gida biyu yayin da ake shirin fitowa titunan Najeriya domin yin zanga-zanga
- Wasu daga cikin malamai sun goyi bayan a fito a yi zanga-zanga wasu kuma suna ganin hakan bai dace ba sam
- Legit ta tattauna da Kwamared Dauda Idris wani dan gwagwarmaya domin jin matsayar da ya dauka daga malaman
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Malamai a Najeriya na cigaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan shirin fita zanga-zanga da matasa ke yi.
An samu rarrabuwar kai tsakanin malamai kasancewar wasu sun goyi bayan lamarin wasu kuma sun nuna bai dace ba.
A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku wasu daga cikin manyan malamai da suka bayyana ra'ayoyinsu a kan fita zanga-zanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malaman da suka goyi bayan zanga zanga
1. Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala, Dakta Ibrahim Jalo Jalingo ya ce tun da dadewa al'ummar Musulmi na yin zanga-zanga.
Dakta Jalo Jalingo ya bayyana haka a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook yana mai cewa babu laifi cikin zanga-zangar lumana.
2. Dakta Ahmad Mahmud Gumi ya yi magana a cikin wani bidiyo da Ameer Sanusi ya wallafa a Facebook cewa a bar matasa su yi zanga-zanga.
Malamin ya ce duk wanda ya ce zai hana zanga-zanga to dole ya dauki mataki kan matsalolin da suka fusata al'umma.
3. Haka zalika Sheikh Muhammad Nuru Khalid ya ce zanga-zanga halal ne a dokar Najeriya saboda haka ya kamata abar mutane su fita.
Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin wani bidiyo da Isiyaku Muhammad Bako ya wallafa a Facebook.
Jerin malaman da suke ƙin zanga-zanga
1. Legit ta ruwaito Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo yana magana kan cewa akwai matsalolin da zanga-zanga zai haifar idan aka fita yinsa.
2. Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya bayyana cewa babu wata musifa da ta fi zanga-zanga girma a wanann lokacin.
Saboda haka ya bayyana cikin wani bidiyo da A.I Mekwabbai ya wallafa a Facebook cewa mutane su hana 'ya'yansu fita zanga-zanga.
3. Babban limanin jami'ar Gombe, Farfesa Dahiru Inuwa Ibrahim ya ja hankalin matasa kan fita zanga-zanga kamar yadda ya wallafa a Facebook.
Legit ta tattauna da Dauda Idris
Kwamared Dauda Idris ya zantawa Legit cewa a matsayinsa na dan gwagwarmaya yana goyon fahimtar bangaren zanga zanga.
Sai dai duk da haka Dauda Idris ya ce shi ba zai samu fita zanga zangar ba saboda wasu dalilai da ba zai iya bayyanawa ga al'umma ba.
Malamai sun yi magana kan sarauta
A wani rahoton, kun ji cewa gamayyar malaman addinin Musulunci da ke jihar Kano sun yi martani kan rawar jami'an tsaro da bangaren shari'a a jihar.
Malaman sun yabawa jami'an tsaro da kuma ɓangaren shari'a kan tabbatar da zaman lafiya a jihar game da rikicin sarauta.
Asali: Legit.ng