El Rufai Ya Dauki Mataki Kan Mamban Majalisar Kaduna da Gidan Jarida, Ya Nemi Diyyar N3bn
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya dauki mataki kan mamban Majalisar jihar Kaduna kan zargin bata masa suna
- El-Rufai ya kuma hada da gidan talabijin na Channels bayan gudanar da hira da Henry Marah kan zargin badakalar N423bn
- Hakan ya biyo bayan kafa kwamitin bincike da Majalisar ta yi domin bincikar gwamnatin El-Rufai daga shekarar 2015 zuwa 2023
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya maka mamban Majalisar jihar, Henry Marah a kotu.
El-Rufai ya kuma hada da gidan jaridar Channels TV domin neman hakkinsa kan zargin badakalar N423bn.
N423bn: El-Rufai ya mamban Majalisar Kaduna
Daily Trust ta tattaro cewa tsohon gwamnan ya dauki matakin ne game da bata masa suna da suka yi kan zargin badakalar da ake yi masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Ministan ta bakin lauyansa, A U Mustapha ya ce hirar da aka gudanar a Channels TV ya saba doka wanda aka bata masa suna ba tare da hujja ba.
Daga bisani El-Rufai ya bukaci biyan diyyar N3bn daga gare su kan kokarin bata suna da suka yi.
Marah ya gudanar da hirar a gidan talabijin na Channels inda ya zargi El-Rufai da karbar bashi ba bisa ka'ida ba.
Zargin da ake yiwa kan El-Rufai
Hakan ya biyo bayan kafa kwamitin bincike da Majalisar jihar ta yi kan tsohon gwamnan da ake zargi da badakalar makudan kuɗi.
Ana zargin El-Rufai ya karkatar da N423bn lokacin da yake mulkin jihar daga shekarar 2015 zuwa 2023 a jihar.
Sai dai El-Rufai da mukarrabansa a lokuta da dama sun sha musanta zargin da cewa akwai bita da kullin siyasa a lamarin.
Majalisar Kaduna ta magantu kan binciken El-Rufai
A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa Majalisar jihar Kaduna ta yi martani kan zargin badakalar N423bn yayin mulkinsa.
Majalisar ta ce ba gudu ba ja da baya kan binciken tsohon gwamnan da ake yi bayan kafa kwamiti a jihar.
Hakan ya biyo bayan martanin tsofaffin mukarraban El-Rufai kan zargin badakala inda suka ce akwai kura-kurai.
Asali: Legit.ng