Kano: Farfesa Mai Matsalar Gani na Farko a Najeriya, Jibril Isa Diso ya Rasu
- Farfesa na farko mai matsalar gani a Najeriya, Farfesa Jibril Isa Diso ya riga mu gidan gaskiya a wannan rana
- Jami'ar Bayero ce ta tabbatar da rasuwarsa a yau Juma'a inda ta yi addu'ar Allah ya gafarta masa
- Dalibansa sun shiga jimami, tare da tuna malamin da jajircewa wajen inganta rayuwarsu da gogewa wajen koyarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Kano- Dalibai da malaman jami'ar Bayero sun shiga alhini bayan rasuwar Farfesa mai matsalar gani na farko a Najeriya, Farfesa Jibril Isa Diso. Daraktan yada labari na jami'ar Bayero a Kano, inda Farfesa Diso ke koyarwa, Lamara Garba ya tabbatar da rasuwar malamin ranar Juma'a.
Jami'ar, a wani dan sako da ta saki a shafinta na Facebook ta nuna alhinin rashin Farfesa Diso.
Za a binne Farfesa Diso yau
Daily Trust ta wallafa cewa za a binne Farfesa Jibril Isa Diso yau a masallacin Juma'a na Abdullahi Bin Abbas, Sabon Titi, Gidan Kankara a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin rasuwarsa, Farfesa Diso malami ne tsangayar ilimi, sashen koyar da ilimi na musamman da ke jami'ar Bayero a Kano
Dalibai sun shiga alhini
Tuni dalibai da abokan aikin Farfesa Diso su ka fara nuna alhinin rashin na gaba,wanda da yawa aka kwatanta shi da mai son ci gaban ilimi.
Saifullahi Mukhtar, tsohon dalibi ne ga Farfesa Diso, ya kuma shaidawa Legit cewa ba karamin rashi su ka yi ba.
A kalamansa;
"Mutum ne mutumin kirki jajirtacce kuma mai karfafawa kowa gwiwa, ba wai iya mu masu bukata ta musamman din ba."
Ya ce a lokacin da Farfesan ya zama mashawarcin gwamna Ibrahim Shekarau a kan masu bukata ta musamman, ya bijiro da kudurorin da har yanzu ana cin moriyarsa.
Saifullahi ya kara da cewa.malamin ne ya jajirce har aka amince da ilimin masu bukata ta musamman kyauta a manyan makarantun Kano.
Tsohon shugaban BUK ya rasu
A baya mun ruwaito cewa tsohon shugaban jami'ar Bayero da ke Kano, Farfesa Ibrahim Umar ya riga mu gidan gaskiya
Marigayin, wanda ya shugabanci BUK tsakanin 1979 da 1986, shine shugaban jami'ar na uku.
Asali: Legit.ng