"Ba Ku da Tarbiyya": Sheikh Rijiyar Lemo Ya Caccaki Matasa Kan Zanga Zanga, Ya Nemo Mafita

"Ba Ku da Tarbiyya": Sheikh Rijiyar Lemo Ya Caccaki Matasa Kan Zanga Zanga, Ya Nemo Mafita

  • Yayin da ake ta shirin fita zanga-zanga a Najeriya, Malamin Musulunci, Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya caccaki matasa
  • Rijiyar Lemo ya koka kan yadda matasan da ke zagi da cin mutuncin malamai za su iya kawo sauyi a Najeriya baki daya
  • Ya ce abin takaici ne yadda suka rasa tarbiyya inda ya ce matasa masu tarbiyya ne kadai za su iya kawo sauyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya caccaki matasa kan shirin fita zanga-zanga a Najeriya.

Shehin malamin ya nuna damuwa kan yadda matasa ke yiwa malamai rashin kunya saboda suna kokarin hana su zanga-zangar.

Sheikh Rijiyar Lemo ya caccaki matasa kan zanga-zanga a Najeriya
Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya koka kan yadda matasa suke cin mutuncin malamai saboda zanga-zanga. Hoto: Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Sheikh Rijiyar Lemo ya gargadi matasa

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Bayero? Malamin addini ya fadi wanda ubangiji ke so ya zama sarkin Kano

Shafin karatuttukan malaman Musulunci ne ya wallafa faifan bidiyon malamin yayin hudubar sallar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rijiyar Lemo ya koka kan yadda matasan ke rashin kunya inda ya ce ba su da tarbiyya ko kadan.

Ya ce babu inda matasa marasa tarbiyya za su iya kawo sauyi a ƙasa musamman a irin wannan hali da ake ciki.

"Matasa suna ta gangami a fito a yi zanga-zanga saboda samun sassauci, malamai suna ta jan hankali kan lamarin saboda abun da yake haifarwa."
"Mu karan kanmu a nan zanga-zangar tana cutar da mu saboda yadda ake fasa shaguna da kantuna har ma da zubar da jini."
"Malamai suna jan hankali, matasa suna zarginsu, yaro ya ce an biya ku kudi sai mun yi kaza mun yi kaza."
"Matasan da ke zagin malamai su ke son wucewa gaba domin kawo canji, ta ina wanda ya rasa tarbiyya zai kawo canji a kasa."

Kara karanta wannan

Rashin aikin yi: Ganduje ya ba matasa shawarar abin da za su yi bayan kammala karatu

- Sheikh Sani Rijiyar Lemo

Babban malamin Musulunci ya rasu a Jos

Kun ji cewa an shiga jimami bayan rasuwar babban limamin masallacin Juma'an Jos da ke jihar Plateau.

Marigayin mai suna Sheikh Lawal Adam Abubakar ya rasu ne a yau Alhamis 11 ga watan Yulin 2024 a Jos.

An tabbatar da cewa marigayin ya rasu yana da shekaru 80 a duniya inda ya bar mata uku da 'ya'ya 14 da kuma jikoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.