Sanusi II Ko Bayero? Malamin Addini Ya Fadi Wanda Ubangiji Ke So Ya Zama Sarkin Kano

Sanusi II Ko Bayero? Malamin Addini Ya Fadi Wanda Ubangiji Ke So Ya Zama Sarkin Kano

  • Babban malamin addinin Kirista, Primate Elijah Ayodele, ya yi magana kan rigimar sarautar da ta mamaye jihar Kano da wasu jihohi
  • Shugaban cocin ruhaniya na INRI ya ce ubangiji ne ya lamunce Muhammadu Sanusi II ya zama sarkin Kano domin cigaban jihar
  • Primate Ayodele ya kuma yi ishara da cewa nan gaba kadan za a ga wani babban al'amari, inda za a mayar da masarautun gargajiya hotiho

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - Wanda ya assasa kuma shugaban cocin ruhaniya na INRI, Primate Elijah Ayodele, ya yi magana kan rigimar sarauta da ta mamaye jihar Kano.

Babban malamin addinin ya bayyana cewa tsohon gwamnan CBN, Muhammadu Sanusi II ne wanda ubangiji ya ke so ya zama sarkin Kano.

Kara karanta wannan

"Tuna halacci ke hana ni ɗaukar wasu matakai": Gwamna ga mai gidansa

Primate Ayodele ya yi magana kan rigimar masarautar Kano
Primate Ayodele ya ce ubangiji ne ya zabi Sanui II ya zama sarkin Kano. Hoto: @HrhBayero, @masarautarkan, @primate_ayodele
Asali: Twitter

"Sanusi II ne zabin ubangiji" - Primate Ayodele

Primate Ayodele ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Legas ranar Talata kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban cocin INRI ya ce:

“Sanusi shine mutumin da ya dace kuma wanda Allah ya kaddara ya mulki Kano idan har ana son cigaba samun nasarori a jihar Kano.”

Primate Ayodele ya jaddada cewa, duk da cewa shi ba Musulmi ba ne, amma yana magana ne bisa isharar ubangiji, inda ya cewa abin da ya faru a Kano zai iya shafar sauran yankunan Najeriya.

Fasto ya magantu kan rigimar sarautar Kano

Jaridar Independent ta ruwaito malamin addinin ya ce:

“Ni ba Musulmi ba ne, amma ina magana ne a matsayin dan aiken ubangiji, kuma abin da ke faruwa a Kano zai yi kamari har ya iya shafar kowane bangare na Najeriya.

Kara karanta wannan

"Babu wanda ya san Kwankwaso": APC ta fadi illar da NNPP za ta samu a zaɓen 2027

“Akwai korafe-korafe kan abin da ke faruwa da masarautun gargajiya. Gwamnati ta na so ta rufe bakinsu domin samun karfin ikon mulki, kuma hakan zai sa 'allura ta tono garma'."

"Sauyi a masarautu na zuwa" - Primate Ayodele

Primate Ayodele ya yi gargadin cewa nan gaba kadan za a iya ganin wani babban sauyi a Najeriya, za a zare duk wani iko na masarautun gargajiya ta yadda za su koma tamkar hoto.

“Akwai wani babban al'amari da ke shirin faruwa na musamman inda za a mayar da sarakuna, Obas, Ezes, da sauran masaratu zuwa hotiho.
"Don haka ya kamata sarakuna su hada kai su yi aiki tare, domin masarautun gargajiya a Najeriya na da matukar tasiri.”

Lauya ya fadi sahihin sarkin Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani lauya mazaunin Kano Umar Sa’ad Hassan ya fassara hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan rikicin masarautar Kano.

Lauyan ya ce hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan rikicin masarautar Kano na nufin Muhammadu Sanusi II ba shi ne Sarkin Kano ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.