NYSC: Ginin Bandaki Ya Rufta Kan ’Yan Mata Masu Bautar Kasa Suna Shirin Wanka
- yRahotanni sun bayyana cewa wasu mata masu hidimar kasa a sansanin NYSC dake Emure a jihar Ekiti sun tsallake rijiya da baya
- An ce suna tsaka da shirin yin wanka a safiyar Juma'a ne bangon bandakin ya rufta musu tare da danne su cikin kasa
- Cikin gaggawa, mazan sansanin suka kai masu dauki tare da zakulo matan da ginin ya danne yayin da aka garzaya da su asibiti
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti - Wasu mata masu hidimar kasa da aka tura jihar Ekiti sun sha da kyar a safiyar Juma'a yayin da bangon bandaki ya rufta kansu a sansanin NYSC dake jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa mazan da ke cikin sansanin ne suka yi gaggawar kaiwa matan dauki tare da zakulosu daga kasan ginin.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wasu masu daga cikin 'yan matan suna kwance a asibiti a halin yanzu sakamon jikkatar da suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bangon bandaki ya rufatawa 'yan mata
Wata majiya daga inda abin ya faru, ta bayyana cewa":
“Eh katangar daya daga cikin dakunan kwanan mata masu bautar kasar ce ta ruguje a yau (Juma’a). Bangon bandakin ne ya rufta ciki yayin da suke shirin yin wanka
”Amma abin ya zo da sauki, jama’a sun garzaya zuwa wurin domin zakulo su daga baraguzan ginin. An kwantar da su a asibitin kuma sun samun sauki."
Wani jami'in NYSC da yayi magana da rokon a boye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace mata biyu ne masu bautar kasa da lamarin ya rutsa dasu kuma suna samun sauki.
"An yi ta kiraye-kiraye na ayi gyara" - Jami'i
Ya ce shugabannin NYSC na jihar Ekiti sun sha yin kira na a gyara gidajen kwanan masu bautar kasar da suka lalace amma abin ya ci tura.
Ya yi kira ga iyaye da masu kula da su da kada su firgita kan lamarin, inda ya kara da cewa hakan ba shi da wani mummunan tasiri ga masu bautar kasar.
An ruwaito cewa 'yan bautar kasar sun shiga sansanin ne na tsawon makonni uku domin samun horo kafin daga bisani a tura su wuraren da za su yi wa kasa hidima.
Majiyar Legit Hausa ta tabbatar da iftila'in
Wata mai hidimar kasa da ta bukaci a sakaya sunanta, ta tabbatarwa Legit Hausa cewa bangon bandakin dakunan kwana na mata a sansanin ya fadi.
Majiyar ta ce da safiyar Juma'a ne suka jiyo wata kara mai razanarwa kamar bindiga, inda daga bisani suka je wurin da karar ta fito, suka tarar bangon bandaki ne ya rufta.
"Ya danne wasu mata dake shirin wanka amma mazan sansanin sun yi hanzarin ceto su daga karkashin ginin da ya danne su."
Majiyar ta ce tuni aka garzaya da matan zuwa wani dakin shan magani, amma suna kyautata zaton za a kaisu babban asibiti idan abin ya fi karfin karamar cibiyar kiwon lafiyar.
Gini ya fadawa dalibai suna jarabawa
A wani labari na daban, mun ruwaito cewa gini ya fada kan wasu dalibai dake rubuta jarabawa a Busa Buji dake karamar hukumar Jos ta jihar Filato.
AN gano cewa, iyayen yara sun garzaya makarantar suna kuka da ihun neman taimako yayin da jami'an tsaro suka dira tare da fara aiki.
Asali: Legit.ng